ADC Ta Ɓullo da Sabon Tsari, Ta Gindaya Wa Atiku, Obi da Amaechi Sharadin Neman Takara a 2027

ADC Ta Ɓullo da Sabon Tsari, Ta Gindaya Wa Atiku, Obi da Amaechi Sharadin Neman Takara a 2027

  • Jam'iyyar ADC ta fara duba hanyoyin da za ta bi don tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa cikin sauƙi, ba tare da an samu matsala ba
  • Masu neman takara a inuwar jam'iyyar haɗaka watau ADC, Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi da Peter Obi za su rattaɓa hannu kan yarjejeniya
  • Wannna yarjejeniya ta tanadi cewa ƴan takarar za su marawa duk wanda ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa baya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Masu neman takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin haɗakar jam’iyyar ADC za su rattaba hannu kan wata yarjejeniya gabanin zaɓen fidda gwani.

Rahotanni sun nuna cewa masu neman takarar za su sa hannu kan yarjejeniyar cewa sun amince za su marawa duk wanda ya lashe tikitin shugaban ƙasa na ADC baya.

Atiku Abubakar, Amaechi da Peter Obi.
Atiku, Obi da Amaechi za su rattaɓa hannu kam yarjejeniya kafin zaben fidda ɗan takarar ADC Hoto: Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi, Peter Obi
Source: Twitter

Leadership ta gano cewa wannan yarjejeniya ce da aka cimma a matakin farko tsakanin ’yan takarar, amma ɗa sharaɗin shirya zaɓe sahihi, na gaskiya da adalci.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun fara nuna wanda suke so jam'iyyar haɗaka ADC ta tsayar takara a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon Ministan Sufuri kuma ɗaya daga cikin jagororin haɗaka, Rotimi Amaechi, ne ya bayyana hakan cikin wata hira ta musamman.

Manyan ƴan takara 3 da ke neman tikitin ADC

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna sha’awar tsayawa takara a 2027 lokacin da ya karɓi baƙuncin wasu jagororin Gombe a gidansa da ke Abuja a makon da ya gabata.

Haka kuma, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi, a cikin wata hira kwanan nan da Channels tv, ya bayyana shirinsa na sake tsayawa takara.

Obi ya kuma ba da tabbacin cewa cewa bai yi wata tattaunawa da kowa ba dangane da zama mataimakin shugaban ƙasa a 2027.

Bugu da ƙari, Tsohon Ministan Sufuri, Chibuike Amaechi, ya bayyana aniyarsa ta neman tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 a ƙarƙashin tutar jam’iyyar ADC.

Sai dai tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Dumebi Kachikwu, ya zargi sabuwar tafiyar haɗaka da shirin ba Atiku tikitin jam’iyyar daga Arewa.

Kara karanta wannan

2027: ADC ta fadi shirinta kan masu burin takarar shugaban kasa

Wannan zargi ya zo a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan ko mulkin ya kamata ya ci gaba da kasancewa a Kudu ko ya koma Arewa a 2027.

Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi.0
Amaechi ya bayyana shirin ADC na gudanar da sahihin zaben fidda gwani gabanin 2027 Hoto: Rt. Hon. Chibuike R. Amaechi
Source: Facebook

Atiku, Peter Obi da Amaechi za su ƙulla yarjejeniya

Duk da haka, da yake zantawa da jaridar, Amaechi ya bayyana cewa yarjejeniyar goyon bayan duk wanda ya fito za ta dogara ne da fahimtar ma’anar “sahihin zaɓe na gaskiya.”

Tsohon gwamnan Jihar Rivers ya ce:

“Abin da muka amince da shi a matakin farko, shi ne cewa duk wanda ya samu nasara daga zaɓen fidda gwani na gaskiya, kowa zai mara masa baya.
"Amma da fari, dole ne mu zauna mu fayyace me muke nufi da zaɓe na gaskiya, saboda yana yiwuwa wani ya ƙwace tsarin zaɓe kuma ya kira shi da gaskiya.”

Okonkwo ya shawarci ADC ta ba Arewa takara

A wani labarin, kun ji cewa tsohon kakakin kwamitin kamfen Obi/Datti a 2023 ya ce matukar ADC da tsayar da ɗan Kudu takara, cikin sauki Bola Tinubu zai samu nasara a 2027.

Kenneth Okonkwo ya shawarci hadakar jam’iyyun adawa da ta tsayar da ɗan takara mai ƙarfi daga Arewa idan har tana son samun nasara.

Okonkwo ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta lalace, kuma dole a dakatar da ita daga ci gaba da cin karenta babu babbaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262