Farouk Aliyu Ya Shiga Rigimar da Ta Ɓarke Tsakanin Mutanen Tinubu da Buhari a APC

Farouk Aliyu Ya Shiga Rigimar da Ta Ɓarke Tsakanin Mutanen Tinubu da Buhari a APC

  • Makusancin Buhari a siyasa, Farouk Aliyu ya musanta ikirarin cewa Bola Tinubu bai taimaki tsohon shugaba Muhammadu Buhari a 2015 ba
  • Farouk ya saɓawa kalaman Boss Mustapha, ya ce duk da Buhari na da ƙuri'u miliyan 12, bai iya cin zaɓe ba sai da ya haɗu da Tinubu a 2015
  • Sai dai ya ce Buhari ya maida biki a 2023, inda ya musanta zargin cewa tsohon shugaban ya yi ƙoƙarin daƙile Bola Tinubu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Abokin siyasa na tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Farouk Aliyu, ya saba wa ikirarin da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha.

Farouk Aliyu, wanda ya daɗe tare da Buhari ya musanta ikirarin Boss Mistapha dangane da rawar da Shugaba Bola Tinubu ya taka a nasarar Buhari a zaɓen 2015.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura Shettima London duba lafiyar Buhari da ke kwance a asibiti

Shugaba Bola Tinubu da magabacinsa, Muhammadu Buhari.
Farouk Aliyu ya musanta kalaman Boss Mustapha kan nasarar Buhari a 2015 Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

A wata hira da aka yi shi a shirin siyasa a yau na Channels tv jiya Alhamis, Farouk ya ce babu shakka Tinubu ya taimaki Buhari har ya zama shugaban ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rigima ta ɓarke tsakanin mutanen Tinubu da Buhari

Tun farko, Boss Mustapha, a wani taron ƙaddamar da littafi a Abuja ranar Laraba, ya ce Tinubu ba shi ne ya sa Buhari ya zama shugaban ƙasa ba.

A cewarsa, dama tuni Buhari na da ƙuri'u kimanin miliyan 12 na masu kaunarsa, kuma majar jam’iyyun da ta kafa APC bai ƙara masa ƙuri'un da suka wuce miliyan 3 ba.

Farouk Aliyu ya karyata wannan batu na tsohon sakataren gwamnatin Buhari, Mustapha, yana mai cewa ba gaskiya ba ne.

Shin Tinubu ya taimaki Buhari a zaɓen 2015?

Ya jaddada cewa duk da Buhari yana da ƙuri'u miliyan 12, hakan bai wadatar da shi wajen lashe zaɓen shugaban ƙasa ba sai da haɗin gwiwa da Tinubu a 2015.

Kara karanta wannan

'Yan APC sun kaure da juna, an zargi Tinubu da kin Buhari tun a karon farko

“Yayana, Boss Mustapha, ya yi kuskure, saboda ban ma san inda yake a wancan lokacin ba,” in ji Farouk.

Farouk Aliyu ya zargi wasu daga cikin wadanda suka shiga gwamnatin Buhari daga baya da kokarin canza tarihin da ba su sani ba.

Mutanen Buhari na ƙoƙarin ɓoye gaskiya

"Abin takaici, da dama daga cikin waɗanda ake kira masu goyon bayan Buhari a yanzu ba su da hannu a gwagwarmayar da ya yi tun asali.
"Wasu kawai ta hanyar ƙaddara ko sa’a suka sami mukami, amma yanzu suna ƙoƙarin murɗe tarihi,” in ji shi.

Farouk ya bayyana cewa Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen fitowar Buhari a matsayin dan takarar APC da kuma samun nasara a babban zaɓen shekarar 2015, rahoton Punch.

Shugaba Buhari tare da Bola Tinubu.
Farouk Aliyu ya nuna damuwa kan yiwuwar haɗa Buhari da Tinubu faɗa a APC Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Farouk na tsoron haɗa Tinubu da Buhari faɗa

“Tinubu ya taimaka, ya bayar da gudunmawa, ya goyi bayan Muhammadu Buhari wajen samun tikitin takara da kuma cin zaɓe.
"Tinubu ya bi mu kowane lungu da saƙo domin yaƙin neman zaɓe. Don haka bana so a ƙirƙiri matsala tsakanin Buhari da Tinubu, domin babu wata matsala tsakaninsu.”

Kara karanta wannan

Rikici ya ɓarke tsakanin mutanen Tinubu da Buhari, an fara musayar yawu kan zaben 2015

- Farouk Aliyu.

Haka nam ya ƙi aminta da cewa Buhari bai rama wa Tinubu ba a zaɓen 2023, yana mai cewa da Buhari na da niyyar karya APC, da ya yi amfani da hanyoyi da dama da ke hannunsa.

Jonathan ya taɓa tsohuwar gwamnatin Buhari

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan , ya zargi magajinsa, Muhammadu Buhari, da titsiye wasu manyan jami’an gwamnatinsa.

Jonathan ya ce Muhammed Adoke, wanda ya yi aiki a matsayin Antoni Janar agwamnatinsa ya sha wahala a mulkin Buhari saboda rawarda ya taka a cikini OPL-245.

Tsohon shugaban ya taɓo wannan batu ne a jawabin da ya yi a taron kaddamar da littafin da Adoke ya rubuta a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262