"Ku Yi Hattara": Malami Ya Fadi Abu 1 da Zai Iya Rusa Hadakarsu Atiku Kafin 2027
- Gabanin zaɓen 2027, Primate Babatunde Elijah Ayodele ya bayyana cewa "sai da sihiri ne kawai za a rushe wannan kawancen" na ADC
- Ana kallon wannan sabon kawancen na ADC a matsayin babban sauyi a fagen siyasar Najeriya, wanda ke shirya dole APC a zaɓen 2027
- Primate Ayodele ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi ga manema labarai, ciki har da wakilin Legit.ng, a yankin Oke-Afa da ke Legas
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas – Primate Elijah Ayodele, wanda ya kafa cocin INRI Evangelical Spiritual Church a Legas, ya bayyana haɗakar jam’iyyar ADC a matsayin “kudurar ubangiji”.
Legit Hausa ta ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, tare da wasu fitattun ’yan siyasa sun zaɓi ADC a matsayin jam'iyyar kalubalantar APC a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
'APC, PDP, ADC, duk ɗaya ne': Shettima ya tura saƙo ga ƴan adawa ana batun haɗaka

Source: Facebook
Peter Obi zai fice daga hadakar ADC
An ƙaddamar da jam'iyyar ADC a Abuja tare da haɗin gwiwar fitattun ’yan adawa daga jam'iyyu daban-daban, kamar yadda muka ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi a ranar Asabar, 5 ga Yuli, 2025, yayin ƙaddamar da littafinsa na shekara-shekara karo na 31 mai taken “Gargadi ga Kasashe", Primate Ayodele ya yi hasashen cewa Peter Obi na jam’iyyar LP zai fice daga wannan haɗakar.
Wakilin jaridar Legit.ng wanda ya halarci taron ya rahoto Primate Ayodele yana cewa:
“Wannan haɗakar daga Allah ce. Sai dai wani sihiri ne kaɗai zai iya rusa ta.
"Peter Obi zai fice daga wannan haɗakar idan ba a yi taka-tsantsan ba. Idan aka ba shi shawarar ficewa da ba ta dace ba, to ba zai yi nasara ba.”
"Atiku ne kawai dan takarar ADC" - Ayodele
Ya ƙara da cewa:
“Idan Obi ya ce zai fice, to a yi amfani da Rotimi Amaechi (tsohon minista). Kuma babu wanda zai tsaya takara a karkashin jam'iyyar illa Atiku.

Kara karanta wannan
Jam'iyyar haɗaka ADC ta zaɓi ɗan takara tsakanin Atiku, Obi da Amaechi? An samu bayanai
"Amma jam’iyyar APC mai mulki na ganin cewa sun riga sun ci zaɓen 2027 saboda gwamnoni da suke tururuwar komawa cikin jam'iyyar.
"Shugaba Bola Tinubu, ba ka ci zaɓen ba tukuna; ina yi maka gargadi yanzu, na fada maka yadda zaka iya ci zabe, kuma na fada maka yadda za a kayar da kai.
"Abin da na faɗa, ubangiji ne ya faɗa mun. Kuma a haka nake isar da saƙon. Idan ba ku ji daɗi ba, to ku jira 2027 za ku gane.”

Source: Facebook
Gargadin da Primate Ayodele ya yi
Tun daga shekarar 1994, Primate Ayodele ya ce ubangiji yana yin magana da shi a kai, kuma a fayyace ba tare da wani rudani ba.
Ya bayyana cewa littattafansa ba rubuce-rubuce na yau da kullum ba ne, illa dai umarni daga sama ne, abun da yake fada kuma gargadi ne daga ubangiji da suka shafi ƙasashe, shugabanni da rayukan mutane.
“Mutane da dama sun yi ba’a da ƙin yarda da sakonni na, amma yau abubuwan da suke faruwa ne ke nuna gaskiyar abubuwan da na sha fada.
"Kowanne shafi na waɗannan littattafai na ɗauke da ruhaniyya, fahimta da shugabanci ga duk wanda ke neman gaskiya a wannan zamani na wahayi.”
- Primate Ayodele.
Malamin duba ya hango nasarar Atiku a 2027
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani malamin gargajiya, wanda ya yi suna bayan hasashen nasarar APC a 2023, yanzu ya ce Shugaba Bola Tinubu ba zai ci zaɓen 2027 ba.
A cikin wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, an hango malamin yana aiwatar da dubararsa ta gargajiya, yana cewa Atiku Abubakar ne zai zama shugaban kasa a zaben mai zuwa.
Hasashen wannan malami ya haifar da muhawara mai zafi a tsakanin 'yan Najeriya, inda da dama ke sa ido don ganin ko zai sake cika hasashensa kamar a baya.
Asali: Legit.ng
