PDP: Bode George Ya Fadi Abin da Zai Hana Tsayar da Ɗan Arewa Takara a 2027
- Tsohon mataimakin shugaban PDP, Cif Bode George ya bayyana takaicin a kan wadanda ke adawa da tsayar da dan Kudu takara
- Bode George ya bayyana cewa tsayar da dan Arewa zai sabawa tsarin raba madafun iko kuma raini ne ga magabata
- Haka kuma ya soki wadanda suka fice daga PDP domin hada kan 'yan adawa, inda ya ce hakansu ba zai cimma ruwa ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon Mataimakin Shugaban PDP, Cif Bode George, ya yi bayanin wanda suke da sha'awar ya kara da Bola Tinubu a zaben 2027.
Bode George ya bayar da tabbacin cewa jam’iyyar PDP ba za ta tsayar da dan takara daga yankin Arewa a 2027 ba.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Bode George ya ce duk wani yunkuri na tsayar da dan Arewa zai zama cin mutunci ga wadanda suka kafa PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon PDP ya magantu kan 2027
Daily Post ta ce Bode George ya nuna damuwa matuka kan yawan ficewar da wasu daga cikin 'yan jam'iyyar ke yi zuwa na adawa da APC.
Ya zargi Shugaba Bola Tinubu da matsa wa gwamnonin PDP lamba domin su sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
A cewarsa:
“Babu wani yiwuwar cewa jam’iyyarmu za ta tsayar da dan Arewa a 2027. Yin hakan cin mutunci ne ga wadanda suka kafa jam’iyyar, da dama daga cikinsu sun riga mu gidan gaskiya.”
Ya ci gaba da cewa:
“Wadanda ke karya tsarin karba-karba a jam’iyya na cin fuskar magabantasu, saboda wannan raini ne. Marigayi Alex Ekwueme ya tsaya takarar tikitin shugaban kasa a PDP amma bai yi nasara ba.
"Amma hakan bai sa ya rusa jam’iyyar ba. Wannan shi ne abin da ake kira mutum mai tsoron Allah.”

Source: Facebook
Bode ya soki masu barin PDP
Jigon jam’iyyar ya bayyana wadanda ke ficewa daga PDP domin kafa wata kawance da cewa hakansu ba zai cimma ruwa ba.
Ya yi wannan jawabi ne yayin wani taro da reshen PDP na jihar Legas ya shirya domin murnar abin da suka kira 'dawowar martabar jam’iyyar.'Ya ce:
“Ina da wata shawara ga dukkannin wadanda suka fice daga jam’iyya suna cewa za su kafa kawance don kayar da Bola Tinubu.
"A halin yanzu, zan iya tabbatar da cewa Bola Tinubu da tawagarsa na matsa wa gwamnoninmu lamba su koma APC."
Ya shawarci jama'a da su bude idanunsu domin ka da a dukunkunesu a gangamin da ake hadawa kan babban zabe mai zuwa.
'Yan APC da PDP sun shiga ADC
A baya, mun wallafa cewa wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyun adawa da dama sun amince da shiga jam'iyyar hadaka ta ADC a matsayin mafita a 2027.
A taron da ya gudana a Gombe ranar Talata, wakilan ADC da fitattun jiga-jigan jam’iyyun adawa sun karbi 'yan APC da PDP domin kalubatantar Bola Tinubu.
Tsohon Ministan Sufuri kuma jagoran hadakar adawa a jihar, Sanata Abdullahi Idris Umar, ya bayyana cewa ba ya ga kwace mulki, ADC na shirin ceto Najeriya.
Asali: Legit.ng


