'Yan APC Sun Kaure da Juna, an Zargi Tinubu da Kin Buhari Tun a Karon Farko
- Tsohuwar hadimar Muhammadu Buhari ta ce Bola Tinubu bai goyi bayan fitowar Buhari a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa ba a APC
- Lauretta Onochie ta ce kalaman Boss Mustapha sun tabbatar da cewa farin jinin Buhari ne ya taimaka masa samun nasara a zaben 2015
- Kalaman Lauretta Onochie na bayyana cewa duk da rawar da Tinubu ya taka a jam’iyyar ACN, bai taka rawa wajen fito da Buhari ba a APC
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohuwar mai taimakawa shugaba Muhammadu Buhari a ɓangaren kafafen yaɗa labarai, ta ce shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bai mara wa Buhari baya ba kwata kwata.
Lauretta Onochie ta ce Tinubu bai goyi bayan Buhari ba lokacin fitowar sa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a 2014.
Onochie ta fadi haka ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X a ranar Alhamis, inda ta ce lokutan ƙaryar da ake yadawa kan Tinubu ne ya fito da Buhari sun ƙare.
Onochie ta nesanta Tinubu da nasarar Buhari
Onochie ta ce wani jawabi da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya yi, ya nuna cewa farin jinin Buhari ne ya ba shi nasarar takara da shugabanci, ba taimakon Tinubu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarta:
“Duk ƙarya tana da lokacin ƙarewa. Jiya ne lokacin ƙaryar da ake cewa Tinubu ne ya fito da Buhari ta ƙare.”
Ta ci gaba da cewa:
“Na gode Boss Mustapha da ka kawo karshen ƙaryar waɗanda ke ƙoƙarin sake rubuta tarihin Najeriya. Tinubu bai goyi bayan fitowar Buhari ba a 2014. Wannan gaskiya ne.”
Leadership ta wallafa cewa Onochie ta haɗa sakon ta da hoton jaridar Tribune inda aka ambato Boss Mustapha yana cewa:
“Farin jinin Buhari ne ya kawo ƙuri’u miliyan 12.5 a 2015, kuma wannan ne ya ba APC nasara.”
Nasarar Buhari: Me Boss Mustapha ya ce?
A bikin kaddamar da littafin Garba Shehu mai taken According to the President Boss Mustapha ya ce nasarar APC a 2015 ta samo asali ne daga farin jinin Buhari, musamman daga sashen CPC.

Kara karanta wannan
Rikici ya ɓarke tsakanin mutanen Tinubu da Buhari, an fara musayar yawu kan zaben 2015
Ya ce:
“A lokacin, CPC na da jiha ɗaya kacal, amma ƙuri’un da suka taimaka mana sun fito daga CPC ne. Farin jinin Buhari ne ya ba mu ƙuri’u miliyan 12.5.”
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da fadar shugaban kasa ke danganta cewa Tinubu ne ya fito da Buhari a zaben 2015 ta hanyar haɗakar jam’iyyun ACN, CPC da sauransu.
Tun da farko dai jam’iyyar APC ta samo asali ne daga haɗakar ACN, ANPP, CPC da wani ɓangare na APGA.

Source: UGC
Ribadu ya gargari masu sukar Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa Nuhu Ribadu ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu tana kokari sosai.
Ribadu ya ce shugaban kasar ya mayar da hankali kan kawo sauye sauye da suka hada da samar da tsaro a Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa 'yan adawa masu shiga talabijin suna sukar gwamnati ne suka lalata kasar a lokacin da suka samu dama a baya.
Asali: Legit.ng
