'Mun Gane Wayon': ADC Ta Yi Martani kan Zargin Shiryawa Tinubu 'Juyin Mulki'
- Jam’iyyar haɗakar adawa ta ADC ta bayyana takaicin kalaman fadar shugaban kasa da ta ce suna barazana ga zaman lafiya
- ADC ta ce kalaman Bayo Onanuga cewa adawa na shirin kifar da Bola Tinubu ba su da tushe, kuma wani yunkuri ne na takura masu
- Jam'iyyar ta ce abin mamaki ne yadda APC da ta hau mulki a matsayin ƴar adawa ke nuna rashin amincewa da muryoyin adawa a yanzu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Jam’iyyar ADC ta mayar da martani mai zafi ga fadar shugaban kasa kan zargin cewa yan adawa na shirin kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Jam’iyyar ta bayyana mamaki kan yadda mashawarcin shugaban kasa, Bayo Oanuga zai rika furta kalaman da ke barazana ga dimokuraɗiyya da hadin kan kasa.

Kara karanta wannan
ADC ta gano yadda ake damfarar yan Najeriya da sunanta, ta tura gargadi ga jama'a

Source: Facebook
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Onanuga ya ce wasu daga cikin yan adawa na hada baki don kifar da gwamnatin da ya kira mafi tsari a tarihin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martanin ADC ga fadar shugaban kasa
Jaridar The Cable ta wallafa cewa kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana kalaman Onanuga a matsayin yunkurin kirkirar wani labari na bogi don a samu hujjar danniya ga jagororin adawa
A cewarsa:
“Wannan rubutu daga Bayo Onanuga wata dabara ce ta siyasa wanda ke amfani da salon jawo hankali ga abin da babu shi.
"Gwamnatin tarayya da APC ke jagoranta na kokarin gina wata tatsuniyar rikici domin ta danne yan adawa.”
Jam’iyyar ADC ta jaddada cewa babu wani shiri na ta da zaune tsaye daga bangarenta, kuma tana kokarinta na kawo sauyi bisa tsarin dimokuraɗiyya ne kadai.
ADC ta caccaki APC
Jam’iyyar ta zargi APC da nuna rashin juriya ga ra’ayoyin da suka saba da nata, tana mai tunatar da cewa ta samu mulki ne a matsayin hadakar adawa.
Bolaji ya ce:
“Abin mamaki ne yadda jam’iyyar da ta hau mulki a matsayin ƴar adawa ke mamakin ganin wasu suna taka irin wannan rawa a yau.”
Jam’iyyar ta bukaci Shugaba Tinubu da ya dakile irin wadannan kalamai daga hadimansa, tana mai gargadi cewa kalaman na iya tayar da hankula.
Ya kuma shawarci ‘yan Najeriya da su kasance cikin shiri da lura da duk wani yunkuri na tauye muryar adawa da da ke fafutukar neman yanci.

Source: Facebook
ADC ta bukaci kungiyoyin kasa da kasa, gwamnatocin da ke girmama dimokuraɗiyya, da masu kare hakkin dan adam da su sa ido kan al’amuran siyasa a Najeriya.
Kakakin jam’iyyar ya kuma shawarci ‘yan Najeriya da su kasance cikin shiri da lura da duk wani yunkuri na tauye muryar adawa da da ke fafutukar neman yanci. ADC ta bukaci kungiyoyin kasa da kasa, gwamnatocin da ke girmama dimokuraɗiyya, da masu kare hakkin dan adam da su sa ido kan siyasa a Najeriya.
ADC ta musanta naɗa shugabannin jihohi
A baya, kun samu labarin cewa Jam’iyyar adawa ADC ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta kan fitar da sunayen shugabannin jihohi.
Rahotannin da aka fitar a baya sun bayyana jerin sunayen wasu mutane da aka ce kowannensu shine shugaban ADC a daya daga cikin jihohin kasar nan, da Abuja.
Jam’iyyar ta bukaci jama’ar Najeriya da su guji yarda da duk wata sanarwa da ba ta fito daga sahihan hanyoyin sadarwarta ba don gujewa amfani da labaran karya.
Asali: Legit.ng

