Rikici Ya Ɓarke tsakanin Mutanen Tinubu da Buhari, An Fara Musayar Yawu kan Zaben 2015

Rikici Ya Ɓarke tsakanin Mutanen Tinubu da Buhari, An Fara Musayar Yawu kan Zaben 2015

  • Hadimin shugaban ƙasa, Temitope Ajayi ya soki tsohon sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha kan batun nasarar Buhari a 2015
  • Boss Mustapha ya musanta ikirarin da ake yi cewa Tinubu ne ya sa Muhammasu Buhari ya zama shugaban ƙasa a 2015
  • Da yake martani, Temitope Ajayi ya ce Tinubu ne ya taimakawa Buhari ya samu nasara a zaben fidda gwanin APC da aka yi a Legas

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Babban mai bai wa shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Temitope Ajayi, ya maida martani ga tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha.

Legit Hausa ta kawo rahoton cewa Boss Mustapha ya fito ya musanta ikirarin cewa Shugaba Tinubu ya sanya Muhammadu Buhari ya ci zaɓen shugaban ƙasa a 2015.

Kara karanta wannan

Boss Mustapha ya daina ɓoye ɓoye, ya tsage gaskiya kan yadda Buhari ya ci zaɓen 2015

Muhammadu Buhari da Tinubu.
Hadimin Tinubu ya yi fatali da kalaman tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha Hoto: Muhammadu Buhari, Asiwsju Bola Ahmed Tinubu
Source: Twitter

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, hadimin shugaban ƙasa ya soki kalaman Boss Mustapha, yana mai cewa ya yi mamaki da yake koƙarin ɓoye tarihi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Tinubu ya taimaki Buhari a APC

Ya bayyana cewa duk da Buhari na da “ƙuri’un Arewa miliyan 12 da ya saba samu,” ya sha kaye a zaɓukan shugaban ƙasa na 2003, 2007 da 2011 kafin ya samu nasara a 2015.

Ajayi ya ce ba don taimakon Tinubu ba a lokacin zaɓen fidda gwanin APC a filin wasa na Teslim Balogun da ke Lagos a 2014, da Buhari ba zai samu tikitin takarar shugaban ƙasa ba.

A cewarsa, Tinubu ne ya haɗo kan gwamnonin APC da wakilan yankin Kudu maso Yamma suka mara wa Buhari baya, wanda hakan ya sa ya lashe zaɓen fidda gwani a 2014.

Fadar shugaban ƙasa ya soki Boss Mustapha

Kara karanta wannan

Ko gezau: Minista ya fadi fargabar Tinubu kan zaben 2027

Ajayi, wanda ya zargi Boss Mustapha da rashin girmama tarihin da bai daɗe da faruwa ba, ya rubuta cewa:

“Mu bar batun babban zaɓen da Janar Buhari ya ci ya zama shugaban ƙasa a 2015. Babu wata hanya da zai ci wannan zaɓen in har bai zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ba a lokacin.”
“Zai wahala Buhari ya lashe zaɓen fidda gwani na APC da aka yi a filin wasan Teslim Balogun a 2014, ba don Shugaba Tinubu ya agaza masa ba, wanda ya haɗa gwamnonin da wakilan Kudu maso Yamma su goyi bayan Buhari.”
"Tsohon SGF, Boss Mustapha, ya manta da tarihi na kusa-kusa a wurin ƙaddamar da littafi, da wannan furuci da ba shi da amfani.”
Bola Tinubu da Muhammadu Buhari.
Fadar shugaban ƙasa ta ce Tinubu ya taimaki Buhari a zaben fidda gwani a 2014 Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Buhari yana goyon bayan haɗakar ADC?

A wani labarin, kun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin Najeriya, Babachir Lawal ya musanta zargin cewa Muhammadu Buhari na tare da jam'iyyar ADC.

Babachir Lawal, wanda ya yi aiki da tsohon shugaban ƙasa Buhari ya ce kwata-kwata ba shi da alaƙa da haɗakar ƴan dawa watau ADC.

A ƙarshen watan Yuni da ya gabata ne, Babashir ya sanar da ficewarsa daga APC, yana mai cewa ba ba zai ci gaba da zama a jam'iyyar ƴan danniya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262