2027: ADC Ta Fara Gargadin Ƴaƴanta kan Takarar Shugaban Ƙasa bayan Hadaka
- Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar ADC, Sanata David Mark, ya gargadi masu nuna sha’awar takara tun da wuri
- Wasu ƴan ADC sun nuna damuwa kan yadda wasu ke nuna kwaɗayin takara, inda su ke ganin kamata ya yi a gina jam'iyya
- A kan batun tasirin ADC, masani Salihu Yakasai ya ce jam'iyyar na da damar nasara idan ta hada kai da fitattun ‘yan siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Jam’iyyar hadaka ta ADC ta tura muhimmin sako ga 'ya'yanta da ke nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa tun kafin lokaci.
Jam’iyyar ta bayyana cewa ba za ta fifita kowa ba yanzu, domin akwai bukatar a gina jam’iyyar da kyau kafin a fara batun shugabanci a zaben 2027.

Source: Facebook
BBC Hausa a ruwaito cewa shugaban rikon kwarya na ADC na kasa, Sanata David Mark ne ya yi gargadin ganin yadda ake kara samun cece-kuce dangane da zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana samun masu son takara a ADC
Punch ta wallafa cewa fitattun ‘yan siyasa kamar Peter Obi, Rotimi Amaechi da wasu daga cikin makusantan Atiku Abubakar na nuna sha'awar takara.
Lamarin na kokarin tayar da kura a cikin jam’iyyar ADC, inda wasu daga cikin ‘ya’yanta ke kokawa kan yadda wasu jiga-jiganta ke nuna sha’awarsu tun da wuri. Wasu daga cikin yan ADC sun nuna cewa irin wannan mataki na iya janyo rabuwar kai, inda suka ce kamata ya fi a mayar da hankali karfafa hadin kai.

Source: Twitter
Dr. Umar Ardo, ɗaya daga cikin jiga-jigan da suka taka rawar gani wajen kafuwar hadakar jam’iyyar ADC, ya bukaci ‘yan siyasa da su mayar da hankali kan fitar da Najeriya daga matsalolin tattalin arziki da tsaro.
A cewarsa:
“Ya kamata duk wani wanda ya ɗauki ra’ayi a kan cewa Najeriya na cikin ƙunci kuma gwamnatin da take ciki yanzu ba ta nuna alamun za ta fidda ƙasar daga cikin wannan ƙuncin ba, ya kamata a tsaya a tabbatar da mun fitar da kasar daga wannan hali."
An shawarci ADC kan takarar shugaban kasa
Masani kuma mai sharhi a kan harkokin siyasa a jihar Kano, Salihu Yusuf Yakasai, ya shaidawa Legit Hausa cewa ADC tana da damar cin moriyar 2027.
Ya ce ADC za ta iya amfani da damarta domin ta yi nasara, musamman idan ta hada kai da wasu fitattun ‘yan siyasa kamar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso. Yakasai ya jaddada cewa irin wannan hadaka na jam’iyyun adawa da manyan ‘yan siyasa na iya zama babbar barazana ga jam’iyyar mai mulki, APC, musamman idan aka yi amfani da dabarun da suka dace.
Ya ce:
"Hadakar yan siyasa da kuma ƙananan jam'iyyu a karkashin jam'iyyar ADC, wannnan ba karamar barazana ba ce ga ita jam'iyya mai mulki, APC, domin da irin wannan hadakar ne ta haye kan karagar mulkin Najeriya."

Kara karanta wannan
Jam'iyyar haɗaka ADC ta zaɓi ɗan takara tsakanin Atiku, Obi da Amaechi? An samu bayanai
Babachir: 'Babu ruwan Buhari da ADC
A wani labarin, mun wallafa cewa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Injiniya Babachir David Lawal ya ce babu ruwan Muhammadu Buhari da ADC.
Ya kara da cewa tsohon shugaban kasar bai taba nuna sha'awar alaka da ADC na, kuma ko da zai dauko maganar, shi Babachir Lawal zai bukaci ya hakura da batun.
Ya kara da zargin cewa jagororin APC ba su daukar shawara, illa ana amfani da jam'iyyar wajen biyan muradun wasu tsirarun mutane kawai da muzgunawa jama'a.
Asali: Legit.ng

