2027: ADC Ta Fadi Shirinta kan Masu Burin Takarar Shugaban Kasa

2027: ADC Ta Fadi Shirinta kan Masu Burin Takarar Shugaban Kasa

  • Jam'iyyar ADC ta fito ta yi magana kan masu burin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashinta a zaɓen shekarar 2027
  • Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa jam'iyyar ba ta da matsala da masu son yin takarar shugaban ƙasa
  • Ya bayyana cewa suna da burin ganin sun ba kowane dan siyasa dama don hakan shi ne adalci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mai magana da yawun jam'iyyar ADC ta ƴan haɗaka, Bolaji Abdullahi, ya yi magana kan masu son tsayawa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashinta.

Bolaji Abdullahi ya ce jam’iyyar ADC ba ta da wata matsala da wani daga cikin shugabanninta da ke da sha’awar tsayawa takarar shugabancin ƙasa.

ADC ta yi magana kan takarar shugaban kasa
ADC ta ce za ta ba kowane dan siyasa dama Hoto: @PeterObi, @Atiku, @ChibuikeAmaechi
Source: Facebook

Bolaji Abdullahi ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin 'Lunchtime Politics' na tashar Channels Tv a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Lukman ya rabawa Atiku da Obi gardama, ya faɗi wanda ADC za ta tsayar takara a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haɗakar ADC ta fara aiki

Bayan ƙaddamar da ADC a ranar 2 ga Yuli, Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, da kuma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, sun bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027.

An kuma ruwaito cewa Atiku Abubakar, wanda ya jagoranci gamayyar jam’iyyun adawa da ta haifar da samuwar ADC, yana da sha’awar tsayawa takara a 2027.

Ko da yake wasu ƴan Najeriya na ganin irin wannan gogayya tsakanin shugabannin jam’iyyar na iya haddasa rikici, mai magana da yawun jam’iyyar ya ce irin waɗannan buruka ba su da wata matsala a wajen ADC.

Menene shirin ADC kan masu burin takara?

Mai magana da yawun na ADC ya ce kowane ɗan siyasa na da buri, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne jam’iyya ta nuna tasirinta wajen daidaitawa da kuma tsara burin mambobinta.

Kara karanta wannan

Shugaban PDP ya aika da sabon gargadi ga mambobin jam'iyyar

"Wannan dai halin ƴan siyasa ne. Kowanne ɗan siyasa yana da buri ta hanya guda ko wata. Amma abin da ke da muhimmanci shi ne jam’iyya ta iya ɗora iko a kan mambobinta, ta tsara ko ta zaburar da burin kowanne ɗan jam’iyya."
"A ma’anar siyasa ma, wannan ne aikin jam’iyya, haɗa ra’ayoyi da buruka. Saboda haka, ba mu da wata matsala da wani da ke cewa yana son zama shugaban ƙasa ko wani muƙami. Ba shi ne matsalar ba."
Ya ƙara da cewa abu mafi muhimmanci ga ADC shi ne ta gina jam’iyya mai ƙarfi wadda take da gaskiya da adalci, wadda kuma ke ba kowane mamba dama.
"Abu mai muhimmanci shi ne mu gina jam’iyya mai ƙarfi wadda take da ikon daidaita mambobinta. Abu na biyu, mu gina jam’iyya mai gaskiya da adalci da ke ba kowa dama."
"Idan ka ba kowa dama, to hakan zai ƙara darajar tasirin jam’iyya, kuma za ka iya ɗaukar mataki kan duk wanda ya saba dokar jam’iyya."

- Bolaji Abdullahi

Jam'iyyar ADC za ta yi wa 'yan takara adalci
ADC ba ta fargaba kan burin Atiku, Amaechi da Peter Obi na yin takara Hoto: @atiku
Source: Facebook

Yadda ADC za ta fitar da ɗan takara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Salihu Lukman ya bayyana yadda ADC za ta fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar haɗaka ADC ta zaɓi ɗan takara tsakanin Atiku, Obi da Amaechi? An samu bayanai

Jigon na haɗakar ADC ya bayyana cewa za a fitar da ɗan takara ne ta hanyar sahihin zaɓen fidda gwani mai cike da gaskiya.

Sai dai, ya nuna cewa har yanzu jam'iyyar ba ta fara tattaunawa ba kan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng