Boss Mustapha Ya Daina Ɓoye-Ɓoye, Ya Tsage Gaskiya kan Yadda Buhari Ya Ci Zaɓen 2015
- Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha ya musanta ikirarin cewa Bola Tinubu ne ya kai Muhammadu Buhari ga nasara a zaɓen 2015
- Boss Mustapha ya ce ƙuri'u miliyan 3 ne suka ƙaru daga ƙuri'u miliyan 12 da Buhari ya saba samu a Arewacin Najeriya a lokacin zaɓe
- Tsohon SGF ya bayyana hakan ne a wurin kaddamar da littafin da tsohon kakakin shugaban ƙasa, Garba Shehu ya rubuta a Abuja yau Laraba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Batun shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya ɗora Muhammadu Buhari a kujerar shugabancin Najeriya a 2015 ya zo ƙarshe.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya musanta ikirarin Shugaba Tinubu cewa shi ya sanya Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasa a 2015.

Source: Twitter
Mustapha ya ce duk da majar da jam'iyyun adawa suka yi a lokacin wanda ya kai ga kafa APC, ƙuri'u miliyan uku kacal suka ƙaru a ƙuri'un Buhari ya saba samu, jaridar This Day ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce Muhammadu Buhari ya samu ƙuri'u miliyan 15 ne a zaɓen 2015, wanda ke nuna ya samu ƙarin ƙuri'u miliyan 3 daga kuri'u miliyan 12 da ya saba samu a Arewa.
Tinubu ya yi ikirarin ɗora Buhari a mulki
Idan baku manta ba tun a shekarar 2022 lokacin da ake shirye-shiryen zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Tinubu ya ce shi ya ɗora Buhari a kujerar shugabancin Najeriya.
A wani taro da ya yi a Abeoukuta, Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa shi ya zaɓi Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin abokin takarar Muhammadu Buhari kafin zaɓen 2015.
Tsohon SGF ya faɗu yadda Buhari ya ci zaɓen 2015
Sai dai da yake kore wannan ikirari wanda ke neman dawowa a yanzu, Boss Mustapha ya musanta cewa Tinubu ya kai Buhari kan madafun iko a wancan lokacin, in ji Punch.
Tsohon sakataren gwamnatin Buhari ya musanta ikirarin ne da yake jawabi a wurin kaddamar da littafin da Garba Shehu, tsohon kakakin shugaban ƙasa ya rubuta a Abuja yau Laraba.

Source: Facebook
"A zaɓen 2003 da ya fafata da Obasanjo, Buhari ya samu ƙuri’u miliyan 12.7. A zaɓen 2007 da ya fafata da Yar’Adua, ya samu ƙuri’u miliyan 6.6. A 2011, ƙuri’un sun ƙaru zuwa miliyan 12.2.
"Amma idan ka tara jimillar ƙuri’un da suka ba mu nasara a zaɓen shugaban ƙasa a 2015, adadin ya kai miliyan 15.4.
"Don haka, a zahiri, abin da sauran jam’iyyun da muka haɗa da su suka ƙara wa ƙuri’un Buhari da suka kai miliyan 12.2, shi ne ƙuri’u miliyan 3.2 kacal."
- Boss Mustapha.
Babachir Lawal ya soki gwamnatin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya bayyana APC a matsayin jam’iyyar danniya da rashin gaskiya.
Lawal, wanda ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance ranar 29 ga Yuni, ya ce ya dade yana adawa da salon mulkin Shugaba Tinubu.
Ya kara da cewa da akwai da yawa daga cikin manyan APC, har da wasu gwamnoni na aiki a boye wajen ganin Tinubu bai yi tazarce ba.
Asali: Legit.ng

