Babachir Lawal Ya Yi Tone Tone, Ya Yi Magana kan Alakar Buhari da Jam'iyyar ADC
- Tsohon Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya bayyana APC a matsayin jam’iyyar danniya da rashin gaskiya
- Ya ce wannan ce ta sa ya dade yana aiki a boye domin kawo wa jam'iyyar nakasu kafin babban zaben 2027 mai zuwa
- Babachir Lawal ya kuma kara da yin bayani a kan matsayar tsohon shugaba, Muhammadu Buhari a kan ADC
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Babachir David Lawal, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya ya bayyana tsohuwar jam'iyyarsa ta APC da kama karya da danniya.
Lawal, wanda ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance ranar 29 ga Yuni, ya ce ya dade yana adawa da salon mulkin gwamnatin tarayya.

Source: Facebook
A wata hira da ta kebanta ga TVC News, Babachir Lawal ya bayyana cewa APC ba ta taɓa zama jam’iyyar tsintsiya madaurinki daya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babachir: ‘Na dade ina dawa da gwamnati’
Babachir Lawal ya tabbatar da cewa tun kafin ya fice daga APC, yana aiki a sirrance domin kawar da gwamnatin Tinubu.
Ya kara da cewa da akwai da yawa daga cikin manyan APC, har da wasu gwamnoni na aiki a boye wajen ganin Tinubu ya samu matsala.
Ya ce:
"Na dade ina aiki a cikin gida da nufin APC ta kai kasa. Da dama ma suna yi, a sirrance.
"Mutane ba sa iya fadar gaskiya. Idan ka ba da shawara, sai a kai maka hari.'
Ya ce yanayin cikin gida na jam’iyyar APC ya rikide kuma babu dadin zama, wanda ke tilasta wa masu bambancin ra’ayi fita daga cikinta.
Babachir ya shawarci jama’a kan ADC
A kan zargin cewa ADC taron 'yan siyasa masu neman mulki ne kawai, Lawal ya ce 'yan Najeriya su maida hankali kan sakamako, ba sunayen mutane ba.
Ya ce:
“Manufarmu ita ce mu cire gwamnatin da ba ta tabuka komai ba, mu maye gurbinta da wadda ta fi ta. Ba don ramuwar gayya muke yi ba.”

Source: Twitter
Tsohon SGF din ya zargi masu goyon bayan Tinubu da manufofin karkatar da hukumomin gwamnati don biyan bukatun kansu.
Ya ce:
“Gwamnonin da ke goyon bayan Tinubu sun san yana da ikon ture su gefe. Don haka su ne ke neman kare kujerunsu.”
A lokacin da aka tambaye shi ko tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yana da alaƙa da hadakar ADC, Babachir ya musanta hakan kwata-kwata.
Ya ce:
“Buhari ba shi da wata alaka da ADC. Idan har zai fara, ni da kaina zan ba shi shawarar ya nesanta kansa.”
An shawarci ADC kan takarar shugaban kasa
A wani labarin, kun ji cewa Kenneth Okonkwo, tsohon jigo a jam’iyyar LP, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da damar sake lashe zaɓen 2027.
Ya ce hakan za ta tabbata idan ADC ta yi kuskuren tsayar da dan takarar shugaban kasa daga Kudancin kasar nan don bugawa da Tinubu.
Okonkwo ya ƙara da cewa idan har ADC na da gaske tana son karbe mulki daga APC, to babu wata hanya mafi sauki illa tsayar da ɗan takara daga Arewa
Asali: Legit.ng


