ADC: Ƴan Takarar Gwamna 2 Sun Fice Daga Jam'iyyar PDP, Sun Shiga Haɗakarsu Atiku

ADC: Ƴan Takarar Gwamna 2 Sun Fice Daga Jam'iyyar PDP, Sun Shiga Haɗakarsu Atiku

  • Tsofaffin 'yan takarar gwamna a Ondo, Eyitayo Jegede da Agboola Ajayi, sun fice daga PDP zuwa ADC tare da wasu jiga-jigan 'yan siyasa
  • Farfesa Bode Ayorinde ya ce haɗakar 'yan adawa na samun karɓuwa a Ondo, kuma ADC na samun karin mambobi ba tare da ba su kuɗi ba
  • Kennedy Peretei ya ce sauya shekar da suka yi daga PDP zuwa ADC ya zama dole sakamakon halin kaka-ni-kayi da ake ciki a Ondo da Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ondo – Tsofaffin ƴan takarar gwamna biyu na jam’iyyar PDP a jihar Ondo, Eyitayo Jegede da Cif Agboola Ajayi, sun sauya sheka zuwa ADC a hukumance.

Eyitayo Jegede da Cif Agboola Ajayi yanzu sun shiga haɗakarsu Atiku Abubakar da ke neman kalubalantar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

"Zai iya kifar da Tinubu," Momodu ya faɗi wanda ya dace ADC ta tsayar takara a 2027

'Yan takarar gwamna a PDP a jihar Ondo sun sauya sheka zuwa ADC
Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai, da kusoshin 'yan adawa a taron kaddamar da ADC a Abuja. Hoto: @atiku
Source: Facebook

Manyan 'yan siyasa a Ondo sun koma ADC

Sauran manyan jiga-jigan da suka sauya sheƙa zuwa ADC sun haɗa da tsohon sanatan Ondo ta Kudu, Nicholas Tofowomo, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Sauran sun haɗa da tsohon ɗan majalisar wakilai, Farfesa Bode Ayorinde; tsohon shugaban PDP na jihar, Tola Alabere; da tsohon sakataren yaɗa labaran PDP, Kennedy Peretei, da sauran su.

Da yake jawabi a wurin ƙaddamar da ADC a jihar, kodinetan kungiyar hadakar, Farfesa Bode Ayorinde, ya bayyana cewa wannan hadaka tana samun ƙarfi a faɗin ƙananan hukumomin Ondo.

Farfesa Ayorinde ya ce:

“Dukkanin ƙananan hukumomi suna tare da mu. Adadinmu yana ƙaruwa, kuma za mu ci gaba da ƙarfafa wannan hadakar don al'umma su shigo.”

Ya bayyana cewa ƙungiyar haɗakar 'yan adawar ba kudi take rabawa ba, kawai tana mai da hankali ne kan neman amincewar mutane daga tushe da kuma shelantar siyasar haɗaka.

Kara karanta wannan

ADC ta shiga Borno da karfinta, tana wawashe yan PDP da APC gabanin 2027

Ondo: 'Yan takarar gwamna sun koma ADC

Farfesa Ayorinde ya bayyanawa al'ummar Ondo cewa za a rarraba katin zama mamban ADC nan ba da jimawa ba a faɗin mazabu da ƙananan hukumomin jihar.

Jaridar Tribun ta rahoto Ayorinde ya ƙara da cewa:

“Tsoffin ƴan takarar gwamna na PDP a zaɓen 2020 da 2024 — Eyitayo Jegede da Agboola Ajayi — suna tare da mu. Sanata Nicholas Tofowomo, Tola Alabere, da Kennedy Peretei ma suna cikin wannan hadakar.”

Ayorinde ya ce ba ya sha’awarsa rike wani muƙami yanzu, inda ya nemi shugabannin mazabu da su rungumi siyasar haɗaka yayin da jihar ke shirye-shiryen zaɓen gwamna mai zuwa.

“Mun fara da mambobi 25 kacal. A yau, mun fi 300. Wannan yana nuna gazawar jam’iyya mai mulki. Ondo ce za ta fara cin moriyar jam'iyyar ADC.”

- Farfesa Bode Ayorinde.

Sakataren yada labaran PDP a Ondo ya ce 'yan PDP da shugabanninsu sun rikide zuwa 'yan ADC
MAnyan jiga-jigan adawa, Peter Obi, Nasir El-Rufai da Atiku Abubakar sun zabi jam'iyyar ADC. Hoto: @ADCngcoalition
Source: Twitter

Shugabanni da mambobin PDP sun koma ADC

A cikin jawabin nasa, tsohon sakataren yaɗa labaran PDP, Kennedy Peretei, ya bayyana ƙungiyar haɗakar a matsayin wata hanya mai muhimmanci don ceto jihar Ondo daga halin da ta shiga.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Jiga jigai 3 sun nemi ruguza haɗaƙar Atiku, Obi da yan haɗaka a ADC

Peretei ya ce:

“Kun ji Farfesa Ayorinde ya ambaci sunaye. Amma ban da manyan sunayen, gaskiyar magana ita cewa, Ondo na buƙatar sabon canji, ana bukatar canji a Najeriya."

Ya tabbatar da cewa a ƙananan hukumomi biyu, jam'iyyar PDP ta rikide zuwa ADC, yana mai cewa PDP ta rushe a waɗannan yankuna.

Tsohon ministan ya bar PDP, ya shiga ADC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Adamu Waziri, ɗaya daga cikin masu kafa PDP kuma mamba a kwamitin amintattu (BoT), ya fice daga jam’iyyar, ya koma ADC.

A cewarsa, ya yanke wannan shawarar ne saboda yadda PDP ta gaza zama sahihiyar jam’iyyar adawa da za ta tsaya wa al’ummar Najeriya a lokacin da suke cikin matsin rayuwa.

Waziri ya bayyana cewa ADC na da karfin da zai iya karɓar mulki daga APC a zaben 2027, tare da farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar da ya tabarbare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com