Tsohon Makusancin Obi Ya Fadi Yadda ADC za Ta Mikawa Tinubu Nasara a 2027
- Tsohon kakakin kamfen jam'iyyar LP a 2023, Kenneth Okonkwo ya shawarci ADC a kan yadda za ta doke Bola Tinubu a 2027
- Ya bayyana cewa babban kuskuren da ADC za ta yi shi ne tsayar da dan takarar shugaban kasa daga Kudancin kasar nan
- Okonkwo na ganin dan Arewa kadai ke da cancanta da goyon bayan da APC ba za ta yi masa karfa-karfa wajen hana shi nasara ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kenneth Okonkwo, tsohon jigo a LP, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da damar sake lashe zaɓe a shekarar 2027.
Ya bayyana cewa haka zai tabbata ga APC matuƙar jam’iyyar ADC ta tsayar da ɗan takara daga kudancin kasar nan.

Source: Facebook
Okonkwo, wanda ya kasance mai magana da yawun kwamitin kamfen na LP a zaɓen 2023, ya bayyana hakan ne a ranar Talata a hira da Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Okonkwo ya gargadi ADC
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Kenneth Okonkwo ya shawarci hadakar jam’iyyun adawa da ta tsayar da ɗan takara mai ƙarfi daga Arewa.
Ya bayyana cewa wannan shi ne zai zamar masu mafita matukr, idan har tana da niyyar karbe mulki daga Tinubu.
Ya ce:
“Manufata a wannan karon ita ce, zan mara wa ɗan Arewa baya a 2027. Dole ne ya kasance ɗan Arewa da gaba ɗaya yankin ke son marawa baya."
"Idan gaba ɗaya Arewa za ta mara wa Atiku baya, me ya hana? Idan za su goyi bayan Tambuwal, ai hakan ma zai yi."
Amma dole mutum mai cancanta ne, wanda kuma ya taba aiki a gwamnati – hakan zai ƙara masa ƙima. Idan aka haɗa shi da ɗan kudu, zai fi samun nasara.”
Okonkwo ya caccaki Tinubu
Okonkwo ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta lalace, kuma dole a dakatar da ita daga ci gaba da cin karenta babu babbaka a filin zabe.

Source: Twitter
Ya ce:
“Duk wanda ke ba ka shawarar tsayar da sabon ɗan Kudu domin ya fafata da Tinubu wanda shi ma ɗan Kudu ne, to yana ba Tinubu tikitin lashe zaɓen kai tsaye. Idan ka kawo ɗan kudu maso gabas, ko da ya ci zaɓe, za su kwace."
Domin a Najeriya, idan ba ka da goyon bayan masu ƙarfi, ko da ka ci zaɓe, za su kwace maka.
Amma idan ka kawo ɗan Arewa, babu wanda zai matsa masa ya mika nasararsa – domin ba daga yanki ɗaya yake da mai mulki ba.”
ADC ta kafa jagoranci a Jigawa
A baya, mun ruwaito cewa Jam’iyyar ADC) ta kaddamar da shugabancinta a jihar Jigawa, inda ta nada Alhaji Ahmed Mahmud Gumel a matsayin jagoranta.
Alhaji Gumel ya bayyana nadin nasa a matsayin wata dama ta kawo sauyi da zai inganta rayuwar al’ummar Najeriya, da ceto su daga halin da APC ta jefa su.
Sabon jagoran jam’iyyar a Jigawa, Alhaji Gumel, ya bukaci jama’ar jihar da ma daukacin ‘yan Najeriya da su rungumi ADC domin inganta makomarsu.
Asali: Legit.ng


