2027: ADC a Kudancin Najeriya Ta Fadi Matsayarta kan Tsayar da Atiku Takara

2027: ADC a Kudancin Najeriya Ta Fadi Matsayarta kan Tsayar da Atiku Takara

  • Jam’iyyar ADC ta karyata rahotannin da ke cewa an bukaci Atiku Abubakar ya janye aniyar neman takarar shugaban kasa a 2027
  • Kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya ce ba a taba yin irin wannan taro ba kuma babu wani tattaunawa a kan haka
  • Ya bayyana cewa a yanzu haka abu daya ne a gabansu, shi ne tattara karfinsu waje guda don tunkarar APC a zabe mai zuwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Jam’iyyar ADC ta musanta rahotannin da ke yawo cewa wasu jiga-jigan siyasa daga yankin Kudu sun yi magana kan tsayar da Atiku Abubakar takara.

Rahotannin sun ce an bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da ya janye niyyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar haɗaka ADC ta zaɓi ɗan takara tsakanin Atiku, Obi da Amaechi? An samu bayanai

Jagororin ADC a yayin taro a Abuja
ADC ta yi magana kan hana Atiku takara Hoto: ADC Coalition 2027
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa wadannan jiga-jigan sun bayyana cewa suna son Atiku ya mara wa dan takara daga Kudancin kasar nan baya a zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya magantu kan takara a 2027

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa an bayyana Atiku Abubakar ya ki amincewa da bukatar da aka gabatar masa a wani taron sirri.

Ya ce:

“Ba zan lamunci matsin lamba da zai sa in hakura da hakkina na doka wajen neman kujerar shugaban kasa ba.
"Kowa da kowa da ya cancanta ya fito, mu gwada farin jininmu a zaben fidda gwani. Bai kamata a rika amfani da tsarin yanki wajen danne cancanta ba.”

ADC ta karyata hana Atiku takara

A jawabinsa ranar Talata, Bolaji Abdullahi, kakakin jam’iyyar ADC, ya ce babu gaskiya a cikin rahotannin, inda ce babu inda aka gudanar da wannan taro.

Ya ce:

“Babu wani da ke tattaunawa kan wannan magana.”

Kara karanta wannan

ADC ta gano shirin gwamnatin Tinubu na ruguza hadakar 'yan adawa a jihohi

Bolaji Abdullahi ya kara da cewa jam’iyyar ADC ta mayar da hankali ne kacokan wajen gina jam’iyyar domin fuskantar zaben 2027.

Makusancin Atiku ya musanta taro kan takara

Wata majiya kusa da Atiku ma ta yi watsi da rahoton, inda ta bayyana shi a matsayin labari kanzon kurege kuma marar tushe ko makama.

Alamar jam'iyyar ADC
An zargi magoya bayan Obi da yada labarin karya kan Atiku Hoto: ADC Coaltion 2027
Source: Twitter

Majiyar ta ce:

“Wa ya jagoranci taron? A ina aka yi taron? Wa da wa ne suka halarta? Wannan duk labari ne na bogi da kuma yada jita-jita.”
“Ko amsa wa irin wannan rahoto tamkar amincewa da shirme ne.”

Majiyar ta zargi magoya bayan Peter Obi da wasu daga cikin jam’iyyar APC da shirya wannan rahoto domin tayar da hankula a cikin jam’iyyar ADC.

ADC ta fara yiwa 'yan adawa barna

A wani labarin, mun ruwaito cewa yayin da shirye-shiryen babban zaɓen 2027 ke kara daukar zafi, jam’iyyar ADC na kara samun karfi a jihar Borno.

Rahotanni daga Borno sun tabbatar da cewa ana samun sauya sheka sosai daga wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa da kuma daga jam’iyyar APC zuwa ADC.

An fara hasashen Kashim Ibrahim Imam, tsohon dan takarar gwamna a PDP kuma jigo a jam’iyyar APC, ya sauya sheka kwanaki masu zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng