Jam'iyyar Haɗaka ADC Ta Zaɓi Ɗan Takara tsakanin Atiku, Obi da Amaechi? An Samu Bayanai

Jam'iyyar Haɗaka ADC Ta Zaɓi Ɗan Takara tsakanin Atiku, Obi da Amaechi? An Samu Bayanai

  • Muƙaddashin shugaban ADC na ƙasa, Sanata David Mark ya ce jam'iyyar ba ta da ɗan takarar da take so daga cikin masu neman tikitinta
  • Atiku Abubakar, Peter Obi da Rotimi Amaechi sun nuna sha'awar neman tikitin takarar jam'iyyar haɗakar a zaben 2027
  • David Mark ya buƙaci ƴan ADC su haɗa kansu wuri guda kafin fara maganar neman kujerar siyasa a zaɓe mai zuwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa babu wani ɗan takara da ta fi so a cikin masu neman tikitin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Shugaban ADC na rikon kwarya kuma tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark ne ya bayyana hakan, ya ce babu wani da suke fifitawa.

Sanata David Mark, shugaban ADC na ƙasa.
Shugaban ADC na kasa ya ce ba su da wani ɗan takara da suka fi so a zaɓen 2027 Hoto: @SenDavidMark
Source: Twitter

David Mark ya bayyana haka ne a wani taro da ya yi da jiga-jigan jam’iyyar ADC na reshen Jihar Kogi a Abuja ranar Talata, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Zai iya kifar da Tinubu," Momodu ya faɗi wanda ya dace ADC ta tsayar takara a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ADC ta zaɓi ɗan takarar tsakanin Atiku, Obi?

Ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa a ƙarƙashin jagorancinsa, jam’iyyar haɗakar watau ADC za ta kasance mai gaskiya da adalci.

"Jam’iyyar ADC ba ta da wani ɗan takara na musamman ko wanda ta fi so a zaben shugaban ƙasa mai zuwa.
"Amma abin da muka mayar da hankali a kai shi ne gina dandalin da zai kasance abin sha’awa kuma wanda mafi yawan ‘yan Najeriya za su karɓe shi hannu biyu.
“Muna wannan ƙoƙari ne saboda ba ma son wannan ƙasa ta mu mai albarka, Najeriya ta nutse, idan muka gaza tashi tsaye yanzu to babu makawa za ta nutse, kowa a cikinmu zai ji jiki.”

- David Mark.

David Mark ya ce ADC jam'iyya ce ta kowa

Muƙaddashin shugaban ADC ya ƙara da cewa dukkan membobin jam’iyyar suna da dama iri ɗaya ta kowane fanni, babu wanda za a fifita kan wani, in ji Daily Trust.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Jiga jigai 3 sun nemi ruguza haɗaƙar Atiku, Obi da yan haɗaka a ADC

Mark ya ce ADC jam’iyya ce mai niyyar gudanar da gaskiya da adalci bisa tsarin dimokuraɗiyya, yana mai ƙarfafa cewa lokaci ya yi da dukkan ‘yan Najeriya za su ɗauki ADC a matsayin "tamu duka."

ADC ta musanta zaɓar dan takara.
Shugaban ADC ya bukaci mambobi su haɗa kai domin tunkarar zabe mai zuwa Hoto: @Atiku
Source: Twitter

Ya kuma ja hankalin mambobi su manta da sabanin ra’ayi, su haɗa kai su gina jam’iyyar kafin a fara maganar burin siyasa.

“Dole ne mu zama tsintsiya madaurinki ɗaya domin gina jam’iyyar kafin mu fara tunanin matsayi ko kujerar siyasa," in ji shi.

David Mark ya kuma bukaci ‘yan siyasa su daina cin mutuncin juna, su mai da hankali wajen warware matsalolin da ke addabar ƙasa, musamman matsalar tsaro, wanda ya ce ADC za ta magance idan ta hau mulki.

2027: Momodu ya faɗi wanda ya fi so a ADC

A wani labarin, kun ji cewa ɗan jarida, Dele Momodu ya ce Atiku Abubakar ne ya fi dacewa haɗakar ƴan adawa ta tsayar takarar shugaban ƙasa a 2027.

Momodu ya jaddada cewa duk da alaƙar abota da ke tsakaninsa da ɗan takarar LP a 2023, Peter Obi, hankalinsa ya fi kwanciya idan aka tsayar da Atiku.

A cewarsa, tsohon mataimakin shugaban ƙasar shi ne madugun adawa, wanda ke da ƙarfin da zai ragargaji APC da Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262