Hadimin Tinubu Ya Fadi Damar da Atiku Ya Rasa Ta Zama Shugaban Kasa

Hadimin Tinubu Ya Fadi Damar da Atiku Ya Rasa Ta Zama Shugaban Kasa

  • Hadimin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wasu kalamai kan tsohon ubangidansa, Alhaji Atiku Abubakar
  • Daniel Bwala ya bayyana cewa wataƙila Atiku ba zai taɓa cika burinsa na zama shugaban ƙasan Najeriya ba
  • Hakazalika ya soki haɗakar ƴan adawa inda ya nuna cewa ba za su daɗe ba rikici zai ɓarke a tsakaninsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hadimin shugaban ƙasa, Daniel Bwala, ya yi magana kan tsohon ubangidansa, Atiku Abubakar.

Daniel Bwala ya bayyana cewa wataƙila tsohon mataimakin shugaban ƙasan ba zai taɓa zama shugaban Najeriya ba duk da shekarun da ya shafe yana fafutukar neman kujerar.

Bwala ya yi magana kan Atiku
Daniel Bwala ya ce watakila Atiku ba zai zama shugaban kasa ba Hoto: @Danielbwala, @atiku
Source: Twitter

Daniel Bwala ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana a cikin shirin 'Politics Today' na tashar Channels Tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me hadimin Tinubu ya ce kan Atiku?

Bwala wanda ya kasance mai magana da yawun Atiku a lokacin zaɓen 2023, ya ce da alama Atiku ya gama amfani da duk damar da zai iya samu don cimma burinsa na zama shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

"Zai iya kifar da Tinubu," Momodu ya faɗi wanda ya dace ADC ta tsayar takara a 2027

"Bisa gaskiya, na bayyana ra’ayina cewa wataƙila Allah bai kaddara masa zama shugaban Najeriya ba, domin ya yi duk abin da ya kamata a yi amma bai lashe zaɓen shugaban ƙasa ba.”
“Shekarar 2023 ita ce babbar damar da tsohon ubangidana Atiku Abubakar ya samu. Ba zai sake samun irin wannan damar ba."

- Daniel Bwala

Daniel Bwala ya caccaki haɗakar ƴan adawa

Bwala ya kuma yi fatali da yiwuwar nasarar sabuwar haɗakar jam’iyyun adawa da suka haɗa da ɗan takarar jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, da kuma tsohon jigo a APC, Rotimi Amaechi, wajen kayar da Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Ya soki yadda ƙawancen ya zaɓi jam’iyyar ADC a matsayin dandalin siyasarsu, yana cewa babu wasu kwararan manufofi ko tsari na daban da suke fitarwa.

“Abin da har yanzu ke ba ni mamaki shi ne, wannan haɗakar ta ƴan siyasar da suka rasa matsuguni ba su da ƙarfin gwiwar fitar da manufofi da suka bambanta ko shirye-shirye na yin gyara."

- Daniel Bwala

Daniel Bwala ya yi magana kan Atiku
Bwala ya ce hadaka za ta wargaje Hoto: @atiku
Source: Facebook

Daniel Bwala ya kuma yi hasashen cewa haɗakar za ta rushe cikin watanni shida saboda rikicin ƙarfi da iko dangane da wanda zai zama ɗan takarar shugaban ƙasa daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Peter Obi ya fadi tagomashin da Arewa za ta samu idan ya yi nasara

Ya ambaci wata magana da Datti Baba-Ahmed ya yi, inda ya bayyana cewa babbar barazana ga haɗin kan haɗakar ita ce burin da kowane daga cikinsu ke da shi na son zama shugaban ƙasa.

“Ɗaya daga cikinsu, sunansa Datti (Baba-Ahmed), ya riga ya hango haɗarin da ke gabansu. Ya ce matsalar wannan haɗaka ita ce wanda zai zama shugaban ƙasa, domin a cewarsa, ‘kowa yana so ya zama shugaban ƙasa’."

- Daniel Bwala

An buƙaci ADC ka da ta ba Atiku takara

A wani labarin kuma, kun ji cewa abokin takarar Peter Obi a zaɓen 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed ya ba jam'iyyar ADC shawara.

Datti Baba-Ahmed ya buƙaci jam'iyyar ADC da ka da ta yi kuskuren ba da tikitin takararta ga Alhaji Atiku Abubakar.

Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana cewa idan aka ba Atiku takara, cikin sauƙi jam'iyyar APC za ta kayar da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng