Tsohon Mataimakin Gwamna Ya Zama Jagoran ADC a Jigawa, an Fara Gangami
- Jam'iyyar ADC na ci gaba da kokarin kafuwa a kokarinta na kalubalantar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027
- ADC ta kaddamar da shugabancinta a Jigawa inda ta dauko tsohon mataimakin gwamna a matsayin jagoranta a jihar
- A jawabinsa, sabon jagoran, Alhaji Ahmed Mahmud Gumel ya shawarci yan ADC da matasan Najeriya a kan su jajirce don watsar da APC
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Jigawa – Jam’iyyar ADC ta kaddamar da shugabancinta a jihar Jigawa tare da nada tsohon mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Ahmed Mahmud Gumel, a matsayin jagoranta.
Gumel ya bayyana cewa jam’iyyar ta ADC ta dauko aniyar dora Najeriya a kan hanyar ci gaba da tabbatar da adalci ga kowa.

Source: Facebook
Jaridar The Guardian ta ruwaito Alhaji Ahmed Mahmud Gumel kara da cewa wannan dama ce ta kawo sauyi da zai inganta rayuwar al’umma a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ADC na neman kafuwa a Jigawa
Joshua Teryila Tarhule ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki a Jigawa sun fara nuna goyon baya ga jam’iyyar.
A cewar rahoton, sabon jagoran, Alhaji Gumel ya bukaci jama’ar Jigawa da daukacin ‘yan Najeriya da su hada kai da ADC don gina makoma mafi inganci ga kasa.
Gumel ya bayyana cewa ADC na zama wata mafita ga ‘yan Najeriya da suka gaji da salon mulkin gwamnatin yanzu, saboda haka ne ma suke samun karbuwa.

Source: Twitter
Ya nanata cewa hadakar da ADC ke yi na samun karbuwa a matakin kasa, inda kungiyoyi da dama da kuma mutane daban-daban ke sauya sheka zuwa jam’iyyar.
Ya ce:
“Shugabannin jam’iyyar sun karɓi wannan ci gaba da hannu biyu, suna mai jaddada aniyarsu na kafa tsarin dimokuraɗiyya mai inganci da ke tattare da kowa da kowa.”
Jagoran ADC ya shawarci yan jam'iyya
Sabon jagoran ADC a Jigawa ya roki mambobin jam’iyyar da su guji zagin shugabanni ko da suna cikin gwamnati ne ko a’a.
Ya kara da cewa:
“Irin wannan hali ba ya cikin akidar zaana mantakewa da siyasar mu, haka kuma hadakar da muke yi ba domin yaki da gwamnatin kama-karya ta APC ba ce, amma domin ceto kasa.”
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya, musamman matasa, da su ci gaba da addu’a da bayar da goyon baya ga wannan hadaka da jam’iyyar ke jagoranta domin ganin an ceto kasar daga halin da take ciki.
ADC ta shiga Borno da karfinta
A wani labarin, kun ji cewa yayin da ake kara matsa shirye-shiryen babban zaɓen 2027, jam’iyyar ADC na samun wurin zama a jihar Borno gabanin zaben 2027 mai zuwa.
Rahotanni sun nuna cewa ana samun sauya sheƙa sosai daga jiga-jigan jam’iyyun adawa da ma daga cikin jam’iyyar mai mulki ta APC, suna tattara na su ya nasu zuwa ADC.
A jihar Borno, Alhaji Idris Mamman Durkwa, wanda ya taba neman tikitin gwamna, da wasu manyan a PDP da LP tuni suka sauya sheka zuwa ADC.
Asali: Legit.ng

