Wata Sabuwa: Gwamna Radda Ya Yi Fallasa kan Hadakar 'Yan Adawa
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya taso jagororin tafiyar haɗakar ƴan adawa a gaba
- Dikko Radda ya bayyana cewa ƴan haɗakar suna surutu ne kawai saboda ba su samu gurbi ba a cikin gwamnati
- Gwamnan ya ƙalubalance su kan su fito su gayawa duniya abin da za su yi daban wanda ya bambanta da irin na gwamnatin APC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya yi watsi da haɗakar jam'iyyuun ƴan adawa.
Gwamna Radda ya bayyana masu jagorantar haɗakar a matsayin waɗanda ke jin haushi kawai saboda ba su cikin gwamnati.

Source: Facebook
Gwamna Radda ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Sunrise Daily' na tashar Channels Tv.
An kafa haɗakar ƴan adawa
Haɗakar ƴan adawan wacce aka sanar da kafuwarta, sun zaɓi jam'iyyar ADC a matsayin dandalin tafiyarsu, bayan watanni ana tattaunawa.
Sun naɗa tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, a matsayin shugaban riko na ƙasa, tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, a matsayin sakatare; da kuma tsohon ministan wasanni, Bolaji Abdullahi, a matsayin mai magana da yawun tafiyar.
Me Radda ya ce kan haɗakar ƴan adawa?
“Mu fuskanci gaskiya. Mu faɗa wa kanmu gaskiya. Lokacin yaudarar ƴan Najeriya ya ƙare. Waye ne bai taɓa kasancewa a gwamnati a mulkin da ya gabata ba? Waye ne ba ya cikin gwamnati yanzu? Mun san tarihin kowa da kowa."
“Mun san abin da suka aikata lokacin suna cikin gwamnati, yanzu kuma suna kuka da kururuwar siyasa domin ba su da wata kujera a gwamnati."
- Gwamna Dikko Radda
Gwamna Radda ya ƙalubalanci ƴan haɗaka
Gwamna Radda ya buƙaci ƴan haɗakar da su fito fili da ajandarsu ga Najeriya, su kuma tallata kansu ga ƴan ƙasa.

Source: Facebook
"Mu daina ruɗar juna. Idan har za mu zo da wani sabon tsari ko mafita ga ƴan Najeriya, tabbas za su rungume shi."
"Su waye ne waɗanda ke cikin wannan haɗakar? Me ya sa ba su shiga wata haɗakar tun da farko ba? Me za su zo su yi daban da abin da ake yi yanzu? Za su iya alƙawarta wa ƴan Najeriya abin da za su yi?”

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Jiga jigai 3 sun nemi ruguza haɗaƙar Atiku, Obi da yan haɗaka a ADC
"Su fito su faɗa wa ƴan Najeriya waɗanda ke da niyyar tsayawa takarar shugabancin ƙasa. Su fito su bayyana, shin za su dawo da tallafin man fetur?"
"Idan har za su dawo da tallafin, to su bayyana wa ƴan Najeriya yadda za su tafiyar da gwamnati? Da wane kuɗi za su gudanar da gwamnati? Kuma da wane kuɗi za su biya tallafin da suke son dawowa da shi?"
- Gwamna Dikko Radda
APC ba ta fargabar haɗakar ƴan adawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta yi magana kan haɗakar ƴan adawa.
APC ta bayyana cewa ko kaɗan ba ta da wata fargaba kan haɗakar ƴan adawan masu son ganin sun kifar da Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Jam'iyyar ta nuna cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗora ƙasar nan kan turbar farfaɗowar tattalin arziƙi.
Asali: Legit.ng
