2027: Fadar Shugaban Kasa Ta Saka Lokacin Wargajewar Hadakar ADC
- Hadimin shugaba Bola Tinubu, Daniel Bwala ya ce hadakar jam’iyyar ADC ba za ta daɗe ba saboda rashin manufa mai karfi
- Daniel Bwala ya ce burin kowa na zama ɗan takara zai haddasa rikici da rugujewar kawancen nan da wata shida
- Bwala ya bayyana cewa babu wata sabuwar dabara daga ADC da za ta iya janyo hankalin masu kada ƙuri’a a 2027
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hadimin shugaba Bola Tinubu, Daniel Bwala ya bayyana cewa hadakar jam’iyyar ADC za ta tarwatse nan da wata shida.
Rahotanni sun nuna cewa Daniel Bwala ya yi maganar ne bayan 'yan adawan Najeriya sun zabi ADC a matsayin dandalin hadaka domin tunkarar Bola Tinubu a 2027.

Source: Facebook
Bwala ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a Channels Television a ranar Litinin, inda ya bayyana rashin daidaiton ra’ayi da son kai a matsayin manyan matsalolin kawancen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce jam'iyyar ba ta da tsayayyen tsarin da zai iya janyo hankalin ‘yan Najeriya kafin babban zaben 2027.
Bwala ya ce hadakar ADC ba ta da makoma
Daniel Bwala ya bayyana cewa jam'iyyar ADC ba ta kawo wani sabon salo ko dabara da za ta iya janyo masu kada ƙuri’a su sauya ra’ayi daga zaben Bola Tinubu zuwa garesu ba.
The Cable ya rahoto Bwala na cewa:
“Ina fada muku magana ta gaskiya, ba da daɗewa ba, wannan kawance ba za a ma ci gaba da tattauna shi ba,”
Me zai jawo tarwatsewar hadakar ADC?
Bwala ya ce kawance irin wannan yana yawan haifar da farin ciki a karon farko, sai daga baya a fara rikici da rarrabuwar kawuna.
Daniel Bwala ya ce:
“Ko wanne daga cikinsu yana son zama shugaban ƙasa. Hakan ne zai haddasa rashin jituwa. Bayan wata daya da kafa kawancen, za ku ga matsaloli sun fara kunno kai,”
Ya ce rikicin shugabanci da burin kowa na zama ɗan takara ne zai fi komai karya wannan haɗaka.
Bwala ya yi hasashen cewa nan da watanni shida, ba za a ma ci gaba da ambaton ADC a matsayin kawancen siyasa ba.

Source: Twitter
'Zaben 2027 zai fi sauki ga APC' – Bwala
A karshe, Bwala ya ce duk da yamutsin da wasu ‘yan adawa ke yi, rashin tsari a cikinsu zai saukaka wa shugaba Tinubu sake lashe zabe.
Ya kara da cewa abin da ya fi kamata shi ne a yi adawa mai ma’ana, ba kawai kafa kawance ba tare da tushe ko hangen nesa ba.
Legit ta tattauna da Ibrahim Hassan
Wani matashi da ya fita daga PDP zuwa ADC ya zantawa Legit cewa da yardar Allah za su kawo karshen APC a 2027.
Matashin ya ce:
"Suna jin tsoron ADC, amma ba za su fito su nuna hakan a fili ba. Amma duk wanda ya ke harkar siyasa ai ya gano hakan. Za mu yi maganinsu a 2027 da yardar Allah."
An zargi Tinubu da rusa hadakar ADC
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar hadaka ta ADC ta zargi gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da kokarin rusa hadakar su.
Mai magana da yawun 'yan adawar ADC, Bolaji Abdullahi ya ce sun samu rahoton cewa gwamnatin Bola Tinubu ta fara gayyatar tsofaffin shugabanninsu.
Bolaji Abdullahi ya yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya guji duk wani kokari na mayar da Najeriya karkashin jam'iyya daya.
Asali: Legit.ng


