2027: APC Ta Cika Baki kan Hadakar 'Yan Adawa da Ke Son Kifar da Tinubu

2027: APC Ta Cika Baki kan Hadakar 'Yan Adawa da Ke Son Kifar da Tinubu

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta taɓo batun haɗakar ƴan adawa masu son kifar da Bola Tinubu a zaɓen 2027
  • Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na APC ya bayyana cewa ko kaɗan jam'iyyar ba ta da wata fargaba kan haɗakar ƴan adawa
  • Felix Morka ya kuma zargi ƴan adawa da jefa ƙasar nan cikin matsalolin da suka daɗe suna ci mata tuwo a ƙwarya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Felix Morka, sakataren yada labarai na ƙasa na jam’iyyar APC, ya yi magana kan haɗakar ƴan adawa da ke son kifar da Shugaba Bola Tinubu.

Felix Morka ya bayyana cewa jam’iyyarsu ba ta damu da fitowar haɗakar jam’iyyun adawa ba da ke son ganin kifar da Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

APC ta yi magana kan hadakar 'yan adawa
APC ta ce ba ta fargaba kan hadakar 'yan adawa Hoto: @atiku, @DOlusegun, @Peterobi
Source: Facebook

Felix Morka ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a tashar Arise tv a ranar Lahadi, 6 ga watan Yulin 2027.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Peter Obi ya fadi tagomashin da Arewa za ta samu idan ya yi nasara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren yaɗa labaran na APC ya zargi shugabannin haɗaka da suka koma jam’iyyar ADC da jefa Najeriya cikin durƙushewar tattalin arziki da talauci.

APC ba ta damu da ƴan haɗaka ba

A cewarsa, Shugaba Tinubu yana nuna ƙwarewa wajen fuskantar manyan matsalolin Najeriya wanda ba kasafai ake samun irin hakan ba.

"Jam’iyyar APC ba ta cikin fargaba, babu wani dalilin da zai sa mu damu."
"Ba ma cikin fargaba domin shugaban ƙasa na tarayyar Najeriya, wanda shi ne shugaban jam’iyyarmu, yana yin aikin da ƴan Najeriya suka zaɓe shi ya yi."

- Felix Morka

Felix Morka ya ƙara da cewa daga cikin dukkan shugabannin da suka shuɗe, Tinubu ne kaɗai ya hau kujerar shugaban ƙasa tare da niyyar fuskantar manyan ƙalubalen da ke addabar ƙasar nan da cikakken ƙuduri da sadaukarwa.

"Ya nuna ƙarfin gwiwar siyasa wanda babu wani shugaban ƙasa da ya taɓa yi kafin shi, wajen tinkarar waɗannan matsalolin."

Kara karanta wannan

"Ku yarda da ni": Obi ya fara lallaɓa ƴan Arewa, yana neman ƙuri'un doke Tinubu a 2027

- Felix Morka

Ya ce sakamakon gyare-gyaren da Tinubu ya aiwatar sun fara bayyana, koda kuwa sannu a hankali ne.

Hakazalika ya yi watsi da suka daga ƴan adawa inda ya bayyana su a matsayin marasa gaskiya waɗanda tuni sun yanke hukuncin cewa gwamnatin Tinubu ba za ta yi kataɓus ba.

“Tun daga farko-farkon wannan gwamnati, waɗannan mutane da suka haɗa kansu a ƙarƙashin ADC sun fara zagin gwamnati tare da cewa ta kasa cika tsammanin ƴan ƙasa a kanta."

- Felix Morka

APC ta tabo batun hadakar 'yan adawa
APC ta zargi 'yan adawa da durkusar da Najeriya Hoto: @PeterObi, @atiku, @DOlusegun
Source: Facebook

Jam'iyyar APC ta caccaki ƴan adawa

Ya bayyana iƙirarin da adawa ke yi da cewa gwamnatin Tinubu ta gaza a matsayin tsabagen ƙarya, yana mai cewa su ne ma ke da alhakin taɓarɓarewar da Najeriya ke fama da ita.

“Waɗannan su ne masu hannu dumu-dumu wajen jefa Najeriya cikin bala’iɓ da yake bin ta."
“Su ne suka haddasa durƙushewar tattalin arzikin ƙasar nan. Su ne suka assasa cin hanci da rashawa, koma baya da talauci mai muni da ke addabar ƙasar nan."

Kara karanta wannan

Haɗakar su El Rufa'i ta yi babban kamu a Kaduna, Hon. Isah Ashiru ya gindaya sharadi

- Felix Morka

Babachir Lawal ya fice daga APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya raba gari da jam'iyyar APC.

Babachir Lawal ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC a hukumance a cikin wata wasiƙa da ya rubuta.

Ya bayyana cewa zai sanar da jam'iyyar da zai koma domin ci gaba da fafutukar ganin an ceto Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng