Sabon Shugaban APC Ya Ragargaji Atiku da Sauran Masu Hadaka a 2027
- Sabon shugaban APC, Ali Bukar Dalori, ya ce zai haɗa kan ‘ya’yan jam’iyya tare da sasanta rigingimu a matakin jihohi da mazabu
- Ya bayyana cewa haɗewar jam’iyyun adawa ba abin tsoro ba ne kuma ba zai yi tasiri ga jam’iyyar APC mai mulki ba
- Rahotanni sun tabbatar da cewa Dalori ya ce wasu jiga-jigan adawa sun shiga APC ne domin tsoron rasa makoma a siyasarsu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Ali Bukar Dalori, ya ce yunƙurin haɗin gwiwar jam’iyyun adawa ba abin da zai tada hankalin jam’iyyarsu ba ne.
Legit Hausa ta samu rahoton cewa Ali Bukar Dalori ya yi magana yana mai jaddada cewa APC na nan da ƙarfin ta.

Source: Twitter
Dalori, wanda ya karɓi ragamar mulkin jam’iyyar ranar Litinin, ya bayyana haka ne a hirarsa ta farko da BBC bayan kama aiki a ofishin jam’iyyar da ke Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, duk wani yunƙuri na adawa ba zai sauya akalar siyasar ƙasar ba, inda ya ce jam’iyyar APC za ta ci gaba da jan ragamar mulki bisa haɗin kai da shawo kan sabani a cikin gida.
Dalori zai haɗa kan 'yan APC a Najeriya
Ali Dalori ya bayyana cewa babbar manufarsa ita ce tabbatar da cewa ‘ya’yan jam’iyyar suna da haɗin kai daga jihohi har zuwa mazabu da ƙananan hukumomi.
Ya ce zai shiga tsakani domin sasanta duk wata ɓaraka da ke cikin jam’iyyar, yana mai cewa:
“Dole na nuna wa duk ‘yan siyasa na APC cewa zan yi iyakacin ƙoƙarina wajen haɗa su.”
Ya ƙara da cewa zai zauna da su ko ya naɗa wakilai domin ganawa da mambobin da ke da sabani, domin siyasa na buƙatar jituwa da fahimta tsakanin mambobi.

Kara karanta wannan
'Babu hadaka da Atiku,' Peter Obi ya ce zai yi takara a 2027, zai yi wa'adi 1 kawai
Maganar Dalori kan hadakar 'yan adawa
Shugaban APC ya ce duk da yunkurin wasu jiga-jigan adawa na haɗa kai, hakan ba zai canza komai ba a jam’iyyar su mai mulki.
A cewarsa:
“Wannan haɗin gwiwar ba za ta tada mana hankali ba. Mun ɗinke jam’iyyar da zare mai ƙarfi wanda ba zai tsinke ba.”
Dalori ya ce siyasa cike take da canje-canje, kuma APC ta saba da jure irin waɗannan ƙalubalen tun kafin ta hau mulki a 2015 har zuwa yanzu.

Source: Facebook
Dalori ya yi iƙirarin cewa wasu daga cikin fitattun ‘yan adawa da suka sauya sheƙa zuwa APC sun yi hakan ne saboda tsoron rasa makomarsu a siyasa.
APC tana maraba da Rabiu Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta bayyana cewa tana maraba da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso idan zai sauya sheka.
Sakataren yada labaran APC na kasa, Felix Morka ya bayyana cewa kofar su a bude take ga duk wani dan siyasa a Najeriya.
Morka ya bayyana cewa Kwanwaso kwararren dan siyasa ne da yake da 'yancin daukar matakin sauya sheka zuwa APC idan ya so hakan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
