Maryam Shetty Ta Tofa Albarkacin Bakinta kan Murabus ɗin Ganduje daga Shugabancin APC
- Maryam Shetty ta bayyana cewa ba ta yi mamakin murabus din Dr. Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin APC ba
- A cewarta, duk abin da ya yi farko to wata rana ƙarshensa zai zo domin haka Allah Ya tsara rayuwar duniya gaba ɗaya
- Maryam, wacce aka naɗa minista amma aka cire sunanta kafin a tantance ta, ta ce Ganduje ya jima yana jagorantar APC
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Ɗaya daga cikin jiga-jigan APC a Kano, Maryam Shettima, wacce aka fi sani da Maryam Shetty ta tofa albarkacin bakinta kan murabus ɗin Abdullahi Umar Ganduje.
Maryam Shetty ta bayyana cewa murabus ɗin da Ganduje ya yi daga shugabancin APC ba abin mamaki ba ne, domin dama komai na duniya yana da farko kuma yana da ƙarshe.

Kara karanta wannan
Bidiyo: Yadda aka yi waje da hoton Ganduje a sakatariyar APC, mutane sun yi martani

Source: Twitter
Injiniya Kabiru Garba, shi ne ya wallafa martanin Maryam a shafinsa na Facebook, inda ta yi hira da BBC hausa kwanaki kaɗan bayan an samu sauyi a APC.
Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano ya ajiye kujerar shugabancin APC ne ranar Juma'a da ta gabata, 27 ga watan Yuni, 2025.
A cewarsa, ya ɗauki wannan mataki ne saboda kiwon lafiyarsa, lamarin da wasu ke ganin ba shi kaɗai ne dalilin murabus din da ya yi kwatsam ba.
Maryam Shetty ta yi magana kan Ganduje
Sai dai da take martani kan wannan lamari, Dr. Maryam Shetty ta ce dama a duniya, komai yana da farko kuma yana da karshe, Allah ƙaɗai ne ba Shi da ƙarshe.
Maryam, wacce aka ba muƙamin minista amma ba a kai ga rantsar da ita ba, aka canza sunanta, ta ce ajiye muƙamin da Ganduje ya yi ba abin mamaki ba ne.
A cewarta, tsohon gwamnan Kano ya jima yana shugabantar APC kuma dama an saba ganin yadda shugabannin jam'iyyar ke ƙarewa da rikici.
Abin da Maryam ta ce kan murabus din Ganduje
"Duk wani abu, yana da farko, yana da karshe, Allah ne kaɗai madawwami, saboda haka ba abin mamaki ba ne domin a koda yaushe ana dubawa ne a ga mai zai taimaki jam'iyya ya kawo mata ci gaba.
"A jawo mutanen da ake ganin za su ƙarawa jam'iyyar armashi, daraja da mutunci. Shi (Ganduje) Allah Ya ba shi dama, ba kowa ke samun irin haka ba, za ka ga da rigime-rigime za a ɗora wannan, ba a daɗe ba ya sauka.
"Amma shi Dr. Umar Ganduje ai ya ɗan jima, ya taka rawarshi, dama duk wani abu da ya yi sama, zai yo ƙasa, rayuwar ma haka take, don haka ba abin mamaki ba ne.
- Maryam Shetty.

Source: Facebook
Maryam ta ƙara da cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da sauran ƙusoshin gwamnati na ganin lokaci ya yi da za a kawo sauyi a jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan
'Murabus ɗin ya fi masa alheri': Jigon APC ya faɗi wulaƙanci da aka shiryawa Ganduje
Ana zargin an shirya wulaƙanta Ganduje
A wani rahoton, kun ji cewa jigon APC a Kano, Alhaji Alhassan Yaryasa ya yi iƙirarin cewa murabus din da Abdulahhi Ganduje ya yi shi ne mafi alheri a gare shi.
Alhassan ya bayyana cewa an shirya wulaƙanta Ganduje ta hanyar fatattakarsa daga shugabancin APC matuƙar bai bi umarnin fadar shugaban ƙasa ba.
Ya ce Ganduje ya cancanci yabo da girmamawa saboda rawar da ya taka a tsawon watanni 22 da ya yi yana jan ragamar jam'iyyar APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
