Ta Faru Ta Ƙare: PDP Ta Amince da Haɗakarsu Atiku, an Shirya Doke Tinubu a 2027

Ta Faru Ta Ƙare: PDP Ta Amince da Haɗakarsu Atiku, an Shirya Doke Tinubu a 2027

  • Jam'iyyar PDP reshen Kebbi ta sanar da shirinta na shiga duk wata hadakar 'yan adawa don kayar da APC a zaɓen 2027 a jiha da kasa
  • Shugabannin PDP sun ce za su goyi bayan duk wata jam'iyyar haɗaka kai don cire APC daga mulki tare da warware rikicin cikin gida
  • Janar Aminu Bande ya soki matsin tattalin arziki da gwamnatin APC ta kawo a jihar Kebbi da zargin kama manyan 'yan adawa a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kebbi - A ranar 28 ga Yuni, 2025, jam'iyyar PDP a jihar Kebbi ta sanar da shirinta na shiga duk wata ƙawance da aka yi niyyar kafa ta don kayar da jam'iyyar APC a zaɓen 2027.

An bayyana wannan ƙuduri ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Birnin Kebbi, inda shugabannin jam'iyyar suka kudurci aniyar warware rikicin cikin gida.

Kara karanta wannan

Rigimar APC: Ganduje ya yi murabus daga kujerarsa ta shugabancin jam'iyyar

Jam'iyyar PDP a Kebbi ta goyi bayan hadakar 'yan adawa don kawo karshen mulkin APC
Shugabannin jam'iyyar PDP na kasa tare da Atiku Abubakar a Abuja. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

PDP za ta goyi bayan hadakar 'yan adawa

Ibrahim Mera, wani fitaccen jigo a PDP, ya shaida wa Channels TV cewa jam'iyyar za ta goyi bayan duk wani ƙawance da zai iya cire APC daga mulki a matakin jiha da ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa:

"Mun kuma amince da yin babban taron jam'iyyar na jiha nan ba da jimawa ba, bisa amincewar shugabancin jam'iyyar na ƙasa."

Ya sake jaddada jajircewar shugabannin jam'iyyar na tattara goyon baya da ƙarfafa tasirin jam'iyyar a faɗin jihar Kebbi.

Har ila yau, da yake jawabi a taron, shugaban PDP na jihar Kebbi, Usman Suru, ya buƙaci mazauna jihar da su daure da wahalhalun da ake ciki a halin yanzu, yana mai tabbatar musu da cewa akwai kyakkyawar makoma a gaba.

Kiran PDP ga jama'a da sukar gwamnatin APC

Usman Suru, ya kuma jaddada ƙudurin jam'iyyar na farfaɗo da tasirinta a faɗin jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

ADA: INEC ta yi bayani kan yiwa jam'iyyu rajista gabanin 2027

A nasa ɓangaren, ɗan takarar gwamna na PDP a zaɓen 2023, Janar Aminu Bande (mai ritaya), ya soki matsin tattalin arziki da ya yawaita a jihar da kuma a faɗin ƙasar.

Ya kuma soki gwamnatin APC ta Kebbi bisa zargin tsananta wa ƴan adawa ta hanyar kama su ba bisa ƙa'ida ba, inji rahoton The Sun.

Tsohon ɗan takarar gwamnan ya yi alƙawarin goyon bayan duk wata hadaka da ke da niyyar kawar da APC da kuma dawo da ingantaccen shugabanci.

Bande ya bayyana cewa:

"Zan goyi bayan PDP da duk wata hadaka da ke da niyyar kawar da APC da kuma kawo ingantaccen shugabanci a jihar Kebbi da Najeriya."
Shugabannin PDP na kasa sun ki amince da hadakarsu Atiku Abubakar
Gwamnonin jam'iyyar PDP tare da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Matakin PDP na kasa da sauye-sauyen jam'iyya

Matakin PDP ya yi daidai da ƙoƙarin da sauran ƴan adawa ke yi na haɗin kai, yayin da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana wata ƙawance da ta haɗa da jiga-jigan PDP, LP, har ma da wasu ƴan APC don kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Sai dai, shugabancin PDP na ƙasa ya nuna cewa ba shi da hannu a cikin ƙawancen Atiku, yana mai cewa sun fi mai da hankali kan gyare-gyaren matsalolin cikin gida.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kara karfi gabanin 2027, sanatan jam'iyyar LP ya sauya sheka zuwa APC

Sauye-sauyen sheka a kwanan nan sun raunana PDP a Kebbi, inda Sanatocin PDP guda uku—Adamu Aliero, Yahaya Abdullahi, da Garba Maidoki—da kuma uku daga cikin ƴan Majalisar jiha huɗu na PDP suka koma APC a 2025.

Shekarau ya shiga hadakarsu Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau da wasu jiga-jigan 'yan siyasa czgz Arewa sun shiga hadakar 'yan adawa.

A wani taro na kwamitin hadakar da aka gudanar ranar Alhamis, an tsayar da ranar 30 ga Mayu domin yanke shawara kan jam'iyyar hadaka.

Rotimi Amaechi ne ke jagorantar kwamitin duba yiwuwar kafa sabuwar jami'iyyar hadaka, yayin da ake nazari kan amfani da SDP ko ADC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com