Bayan Hasashe da Dama, an Gano 'Dalilin' Murabus Din Ganduje daga Shugabancin APC
- Ana ta hadashe kan dalilin murabus din Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin APC mai mulki a jiya Juma'a
- Wasu sun yi zargin cewa DSS na tuhumarsa da cin hanci, musamman kan zaben Bwari da aka ce an sauya sakamako
- Sannan an ce Bola Tinubu ne ya umarci gwamnonin APC da su “ba da shawara” ga Ganduje ya sauka bayan rahoton DSS
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Bayanai suna kara fitowa kan ainihin dalilin murabus din tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje.
Abdullahi Ganduje dai ya yi murabus daga mukaminsa a ranar Juma’a, abin da aka bayyana da ba a zata ba.

Source: Facebook
Ana hasashen dalilin murabus din Ganduje
Daily Nigerian ta ce an nada Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar a ranar 3 ga Agusta, 2023, bayan murabus da aka tilasta wa tsohon gwamnan Nasarawa, Abdullahi Adamu.

Kara karanta wannan
'An taso Kashim Shettima a gaba': Ƴan Borno sun jefo zargi bayan murabus ɗin Ganduje
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun ce murabus dinsa ya biyo bayan matsin lamba daga yankin Arewa ta Tsakiya, wanda ya haifar da rikicin shugabanci a jam’iyyar.
Sai dai wasu majiyoyi sun ce Shugaba Bola Tinubu ne ya umurce shi da murabus, bayan rahoton DSS da ya zarge shi da cin hanci da rashawa.
Majiyar ta ce abinda ya fi janyo matsin lamba shi ne yadda aka tafka magudi a zaben fidda gwani na karamar hukumar Bwari, wanda ya haddasa mutuwa.
Wani Enyigwe Matthew, ya rubuta a shafinsa na sada zumunta:
“Da irin wannan zabe na APC da na gani a otal na Liberty, Bwari, na tabbatar Ganduje ba zai daɗe a shugabancin jam’iyya ba, ya kori ‘yan takara da ‘yan jarida da ‘yan sanda, ya kuma kawo rigima.”

Source: Twitter
Ana zargin umartar DSS fara binciken Ganduje
Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida cewa shugaban kasa ya umurci DSS da su binciki zarge-zargen rashawa.
Bayan an mika rahoton binciken, an kira shugaban gwamnonin APC, Hope Uzodimma, da hadimin shugaban kasa kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari.
Daga bisani, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya hadu da su suka je suka isar da sakon shugaban kasa ga Ganduje.
Ganduje ya so ganin shugaban kasa a daren Alhamis domin neman damar ci gaba da jagorantar jam’iyya har zuwa taron kasa a watan Disamba.
Amma da safe a ranar Juma’a, bayan ganawa da shugaban DSS, Adeola Ajayi, Ganduje ya gamsu da yin murabus, yana cewa “dalilin lafiyarsa” ne.
APC: An so cire Ganduje tun a bara
Tun kafin hakan, Tinubu ya so cire Ganduje saboda koke-koken cin hanci da rashin adalci da suka fito daga yankin Arewa ta Tsakiya da sauran sassa.
A watan Agusta 2024, an shirya tura Ganduje matsayin jakada, inda Tinubu ya umarci shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya isar da sako gare shi.
Sai dai Ganduje ya nemi Bisi Akande ya shawo kan shugaban kasa domin a bar shi ya jagoranci jam’iyya zuwa Disambar 2025.

Kara karanta wannan
'Ka cika gwarzo': Peter Obi ya yaba da murabus ɗin Ganduje, ya yi masa ruwan addu'o'i
Matsalar Ganduje da Uzodinma, Akume
Ganduje ya samu sabani da abokan tafiyarsa irinsu Hope Uzodinma da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, a cikin jam’iyyar APC.
Uzodinma wanda ya saba goyon bayan Ganduje, yanzu ya marawa shugaban kasa baya sakamakon “tsoma baki” a harkokin APC na Kudu maso Gabas.
A Benue kuma, Ganduje ya bar Akume ya mara baya ga Gwamna Hyacinth Alia, sabanin yarjejeniyar da suka cimma dangane da rikicin jam’iyya.
Yan Borno suna zargin neman dakile Shettima
Kun ji cewa yan jihar Borno sun yi magana bayan murabus din Abdullahi Ganduje daga kujerar shugabancin jam'iyyar APC.
Wasu daga cikin mazauna jihar sun ce an shirya hakan a matsayin wata dabara ce ta hana Kashim Shettima samun tikitin mataimakin shugaban kasa.
Mafi yawansu sun bayyana cewa sauya shugabancin jam’iyyar APC daga Ganduje zuwa Borno zai iya kawo sauyi a tsarin yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
