An Gano Yadda aka Tilastawa Ganduje Yin Murabus daga Shugabancin APC
- Wasu rahotanni sun bayyana cewa an tilasta wa Abdullahi Umar Ganduje yin murabus daga shugabancin jam’iyyar APC
- Rahoton ya ce wasu jami’an tsaro sun ziyarci gidan Ganduje da sassafe ranar Juma’a domin karɓar takardar murabus dinsa
- Wasu majiyoyi sun ce murabus ɗin na da nasaba da shirin komawar Rabiu Kwankwaso zuwa APC gabanin babban zaɓen 2027
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun nuna tilasata wa tsohon gwamnan jihar Kano Abdulahi Umar Ganduje, aka yi ya yi murabus a shugabancin APC.
Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya miƙa takardar murabus dinsa ne ranar Juma’a da yamma, inda ya ambato dalilan lafiya a matsayin hujja.

Source: Facebook
Sai dai jaridar Daily Trust ta gano cewa matakin na da alaka da abin da ke faruwa gabanin babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
'Ka cika gwarzo': Peter Obi ya yaba da murabus ɗin Ganduje, ya yi masa ruwan addu'o'i
Wani jami’in tsaro daga cikin manyan shugabannin jami’an tsaron ƙasa ya kai wa Ganduje ziyara a gidansa da misalin ƙarfe 2:00 na dare, inda aka bukaci ya miƙa takardar murabus.
APC: Ganduje ya yi murabus babu shiri
Wata majiya daga cikin makusantan Ganduje ta bayyana cewa mutanen sun shiga cikin ruɗani da mamaki ganin irin wannan mataki da aka ɗauka cikin gaggawa.
A cewar majiyar:
“Shugaban bai nuna wani alamar cewa zai sauka ba. Dukkanmu abin ya zo mana a bazata,”
A cewar wata majiya ta daban, gwamna daga Arewa maso Gabas da kuma wani fitaccen ɗan siyasa daga Arewa maso Yamma sun ziyarci Ganduje da safe domin nuna alhini bisa lamarin.
A daidai lokacin da ake ci gaba da tantama kan batun, Ganduje ya jagoranci tawagar shugabannin jam’iyyar zuwa ofishin gwamnatin jihar Neja a Abuja domin jaje bisa ambaliyar Mokawa.
Alakar saukar Ganduje da jawo Kwankwaso
Wasu rahotanni sun ce daya daga cikin dalilan murabus ɗin Ganduje shi ne kokarin jawo Rabiu Musa Kwankwaso daga NNPP zuwa APC.
Majiyar ta ce shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na da muradin ganin Kwankwaso ya dawo cikin APC, amma daya daga cikin sharuddan da Kwankwaso ya gindaya shi ne a cire Ganduje.
Rahoton ya kara da cewa:
“Tun da Ganduje ke shugabancin APC, Kwankwaso ba zai iya shiga jam’iyyar a karkashinsa ba. Ana ganin hakan ne ya hana shi komawa APC,”
Baya ga haka, wani rahoto ya kara da cewa bangaren Atiku Abubakar ya riga ya yi wa Kwankwaso magana kan shiga hadakar 'yan adawa.
Daily Post ta ce ana ganin haka ne ya sanya Bola Tinubu gaggawar sallamar Ganduje domin shigo da Kwankwaso kafin ya shiga cikin hadakar 'yan adawa.

Source: Facebook
Gwamnonin APC 23 sun yi taro a Edo
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin APC 23 sun yi taro a jihar Edo domin tattauna batutuwan kasa.
Wani rahoto da jaridar Legit Hausa ta samu ya nuna cewa gwamnonin sun tattauna batutuwan da suka shafi hadin kai da cigaban kasa.
Gwamnonin sun yi taron ne a jihar Edo jim kadan bayan murabus din da shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya yi.
Asali: Legit.ng
