'Ka Cika Gwarzo': Peter Obi Ya Yaba da Murabus Ɗin Ganduje, Ya Yi Masa Ruwan Addu'o'i

'Ka Cika Gwarzo': Peter Obi Ya Yaba da Murabus Ɗin Ganduje, Ya Yi Masa Ruwan Addu'o'i

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya yi magana bayan tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya yi murabus
  • Obi ya yaba wa Ganduje bisa murabus dinsa daga shugabancin jam'iyyar, yana mai cewa hakan abin koyi ne
  • Obi ya ce Ganduje ya dauki matakin da ya dace domin ya fi fifita lafiyarsa sama da duk wani mukami ko matsayi na siyasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi, ya yi martani bayan murabus din Abdullahi Ganduje.

Peter Obi ya yaba wa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, bisa murabus dinsa daga shugabancin APC.

Peter Obi ya yabawa Ganduje bayan murabus
Peter Obi ya bukaci yan siyasa su yi koyi da halin Ganduje. Hoto: Peter Obi, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da tsohon gwamnan Anambra ya wallafa a shafinsa na X a jiya Juma'a 27 ga watan Yunin 2025.

Kara karanta wannan

'Murabus din Ganduje ya bude wa Kwankwaso kofar shiga APC,' Jigon jam'iyya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilan da ake ganin ya tilasta Ganduje murabus

Legit Hausa ta samu labarin murabus din Ganduje a ranar Juma’a wanda lamarin ya sanya shakku kan dalilin murabus din.

Tsohon gwamnan na Kano mai shekara 75 a duniya ya ce dalilin shi shi ne duba lafiyarsa.

Wasu kuma suna ganin hakan yana da nasaba da neman kujerar mataimakin Bola Tinubu, sai dai babu wani rahoto da ya tabbatar da jita-jitar.

Har ila yau, wasu na ganin murabus din na da nasaba da shirin dawowar Rabi'u Musa Kwankwaso zuwa jam'iyyar APC.

Peter Obi ya yabawa Ganduje kan murabus

Obi ya ce Ganduje ya ba da kyakkyawan darasi da shugabanni inda ya ce za su iya koyi da shi.

Ya ce:

“Na karanta rahoton da ke cewa Shugaban jam’iyya mai mulki, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ajiye mukaminsa nan take, yana cewa rashin lafiya ne dalili.

Kara karanta wannan

Abin da ƴan Najeriya ke cewa da Ganduje ya yi murabus daga shugabancin APC

“Dole ne in yaba wa Dr. Ganduje saboda fifita lafiyarsa, idan lafiyarsa na tabarbarewa, janyewar akwai da hikima da kima.
Peter Obi ya yi magana bayan Ganduje ya yi murabus
Peter Obi ya yabawa Ganduje bayan ya ajiye shugabancin APC. Hoto: Peter Obi.
Source: Twitter

Obi: Kalubalen da Ganduje Peter Obi ya jefawa shugabanni

Peter Obi ya kalubalanci yan siyasa su yi koyi da halin Ganduje musamman a lokutan da suke fama da wani yanayi na rashin lafiya.

Ya ce tabbas Najeriya na fama da kalubale wanda ke jawo matsaloli a shugabanci musamman daga yan siyasa da ba su da koshin lafiya.

Ya kara da cewa:

“Da wannan abin da ya yi, Dr. Ganduje ya jefa kalubale ga sauran shugabanni da rashin lafiya ya hana su yin aiki yadda ya kamata.
“Ina fatan za su koyi darasi daga gare shi. Kalubalen da Najeriya ke fuskanta na bukatar shugabanni masu lafiya da kuzari."

Ya ce Najeriya yanzu ba ta bukatar shugabanni masu dogon hutu ko tafiya neman lafiya a waje sakamakon rashin lafiya ko tsufa.

Daga karshe, tsohon gwamnan Anambra ya yi addu’ar Ubangiji ya yi wa ritayar Ganduje albarka.

Jigon APC ya magantu kan murabus din Ganduje

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake ɗauko mutumin Buhari, ya ba shi babban muƙami a gwamnatinsa

Kun ji cewa wani jigo a jam’iyyar APC da ya boye sunansa ya yi hasashen cewa murabus din Abdullahi Ganduje na iya bude kofar shigar Rabiu Kwankwaso.

Jigon ya ce dama Abbdullahi Ganduje na rike ne da kujera ce da aka ware wa yankin Arewa ta Tsakiya, kuma hakan ya yi kokarin kawo rikici.

Dan siyasar ya ce akwai yiwuwar Kwankwaso ya karɓi shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa idan har ya sauya sheka zuwa cikinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.