Gwamnonin APC 23 Sun Gana da Juna bayan Murabus din Ganduje
- Gwamnonin jam’iyyar APC sun gudanar da taron jihohi a ƙarƙashin Progressive Governors’ Forum (PGF) a Benin, jihar Edo
- Taron ya gudana ne sa'o'i kadan bayan murabus ɗin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje
- Gwamnonin sun tattauna batutuwa da suka shafi haɗin kan jam’iyya da inganta mulki a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Edo - Gwamnonin APC 23 sun gana da juna a gidan gwamnatin Edo a daren Juma'a bayan murabus din Abdullahi Ganduje.
Shugaban gwamnonin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya na cikin wandanda suka haarci taron jam'iyyar.

Source: Facebook
Hadimin gwamna Umaru Bago na jihar Neje ne ya wallafa abubuwan da aka tattauna yayin taron a shafinsa na X.
Taron ya samu halartar dukkan gwamnonin APC, inda suka tattauna hanyoyin haɗin gwiwa a tsakanin jihohi, da kuma sabunta kudurin tabbatar da kyakkyawan shugabanci.
Taron na zuwa ne sa'o'i kadan bayan Ganduje ya yi murabus daga kujerar shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa.
An yi taron Gwamnonin APC ƙarƙashin Uzodinma
Gwamna Mohammed Umaru Bago da ya halarci taron a matsayin ɗaya daga cikin gwamnonin APC guda 23, ya bayyana cewa taron ya gudana ne a fadar gwamnatin jihar Edo.
Baya ga haka, ya kara da cewa an yi taron ne a ƙarƙashin jagorancin shugaban kungiyar PGF kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma.
A cewar gwamna Bago, taron na da nufin zurfafa haɗin kai tsakanin jihohi, da karfafa zaman lafiya da cigaba a karkashin manufar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Manufar taron gwamnonin APC a jihar Edo
Gwamnonin sun bayyana aniyar su ta ɗaukar matakai da za su samar da mafita ga matsalolin da suka addabi jihohi daban-daban, ta hanyar musayar ra’ayoyi da dabarun cigaba.
A yayin taron, an jaddada muhimmancin tsayawa tsayin daka wajen sauke nauyin da ke kansu na tafiyar da mulki yadda ya kamata, tare da tabbatar da gaskiya da rikon amana.
Rahoto ya nuna cewa taron ya kasance wata dama ta musamman domin sake duba hanyoyin da za a tallafawa juna tsakanin jihohi.
Hadimin gwamnan Gombe, Ismaila Uba Misilli ya wallafa a Facebook cewa taron ya mayar da hankali kan ciyar da jam’iyyar APC gaba.

Source: Facebook
Alakar taron APC da murabus din Ganduje
Taron ya zo a wani lokaci da jam’iyyar APC ke buƙatar daidaito da sake karfafa tushe, sakamakon murabus da Ganduje ya yi, wanda ya jawo tambayoyi a kan makomar shugabancin jam’iyyar.
Duk da cewa ba wani bayani kan murabus din Ganduje a taron, gwamnonin sun jaddada cewa sun shirya tsaf wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaban APC.
Ana hasashen Kwankwaso zai koma APC
A wani rahoton, kun ji cewa wani jigo a APC ya yi magana bayan murabus din Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Jigon jam'iyyar ya ce hakan ya bude kofa wa babban abokin hamayyar Ganduje a Kano, Rabiu Musa Kwankwaso zuwa APC.
Sai dai duk da haka, kusa a jam'iyyar ya ce ba lallai murabus din Ganduje ya shafi hadin kai da karfin APC a jihar Kano ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

