Mataimaki a 2027: Barau Ya Fadi Shirinsa kan Yin Aiki da Shugaba Tinubu
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi magana kan alaƙarsa da shugaban ƙasa Bola Tinubu
- Sanata Barau ya bayyana cewa yana yi wa Tinubu kallon uba a siyasa kuma duk abin da ya sanya shi zai yi
- Ya nuna cewa bai kamata a fara maganar siyasa tun yanzu ba, domin lokaci ne na sauke nauyin da jama'a suka ɗora kan shugabanni
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya sake taɓo batun wanda zai yi wa Shugaba Bola Tinubu mataimaki a zaɓen 2027.
Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa zai fi so kada a ja shi cikin tattaunawa kan wanda zai iya zama mataimakin Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce Barau ya faɗi hakan ne yayin wani taron manema labarai dangane da shirin sauraron ra’ayoyin jama’a na shiyyar Arewa maso Yamma da kwamitin majalisar dattawa kan sauya fasalin kundin tsarin mulki ke shiryawa.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya yi magana kai tsaye kan Atiku da El Rufai masu shirin kifar da shi a 2027
Sanata Barau zai yi biyayya ga Tinubu
Sanatan ya bayyana cewa zai karɓi kowane nau’in aikin da shugaban ƙasa zai ɗora masa da hannu bibbiyu.
"Duk abin da shugaban ƙasa ya buƙaci na yi, zan yi shi 100%."
- Sanata Barau Jibrin
Wannan jawabi na biyo bayan wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata inda ya shawarci wasu ƙungiyoyi da ke son ya tsaya takarar mataimakin shugaban ƙasa a 2027 da su maida hankali wajen mara wa gwamnatin Shugaba Tinubu baya.
Yayin da yake sake tsokaci a kan batun, Barau ya ce bai kamata a fara maganar siyasa tun yanzu ba.
"Magana a kan wannan batu a yanzu ta yi wuri. Na fada wa waɗancan ƙungiyoyi, gaskiya ban san su ba, amma na gode da yadda suka nuna goyon baya gare ni."
"Sai dai na gaya musu cewa, maimakon ku ɓata lokacinku a kan abin da ba ya da amfani yanzu, ku karkatar da ƙarfinku wajen goyon bayan shugaban ƙasa."
"Lokacin siyasa zai zo. Amma wannan lokacin na shugabanci ne."
- Sanata Barau Jibrin
Barau ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin ubansa a siyasa, wanda yake yi wa cikakkiyar biyayya.
"Shugaban ƙasa shi ne ubana a siyasa. Da za ku san abubuwan da ya yi mani da mutanen jihata, za ku yi mamaki. Don haka duk abin da ya buƙaci na yi, idan lokacin ya yi, zan yi. Ina da cikakkiyar biyayya gare shi."
- Sanata Barau Jibrin

Source: Facebook
Barau Jibrin ya yabi Bola Tinubu
Ya yabawa Shugaba Tinubu bisa yadda ya warware rikice-rikicen jam’iyya a jihar Kano, ya tabbatar da dawowarsa majalisa a 2023, da kuma goyon bayan da ya ba shi har ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa.
"Don haka, idan lokacin ya yi, kuma ya ce, ‘ina so ka yi aiki tare da ni,’ zan ce masa, ‘na gode, ranka ya daɗe,’ kuma zan yi. Duk abin da ya umarce ni da shi, zan yi. Ina da cikakkiyar biyayya gare shi 100%. Shugaban kasa uba ne ga ƙasa, kada a yi kuskure."
- Sanata Barau Jibrin
An fara ruguza hotunan Tinubu a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu matasa sun fara lalata allunan tallar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na zaɓen 2027.
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta fitar da sanarwar gargaɗi ga jama'a kan su guji lalata kadarorin gwamnati.
Sanarwar ta bayyana cewa za a hukunta duk wanda aka samu da hannu a wajen aikata irin waɗannan ayyukan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

