Shiga Tafiyar Hadaka: Ndume Ya Fadi Dalilin da Zai Sa Ya Fice daga Jam'iyyar APC

Shiga Tafiyar Hadaka: Ndume Ya Fadi Dalilin da Zai Sa Ya Fice daga Jam'iyyar APC

  • Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a yi magana kan shiga tafiyar haɗakar shugabannin ƴan adawa
  • Ndume ya bayyana cewa akwai yiwuwar zai iya ficewa daga jam'iyyar APC idan Shugaba Bola Tinubu ya gaza sauke nauyin da ke kansa
  • Sai dai 'dan majalisar ya nuna cewa har yanzu yana da fatan cewa shugaban ƙasan zai gyara al'amura a ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, ya yi magana kan ficewa daga jam'iyyar APC.

Sanata Ali Ndume ya ce zai iya ficewa daga jam’iyyar APC idan Shugaba Bola Tinubu ya gaza gyara al’amuran ƙasar nan.

Ndume ya tabo batun ficewa daga APC
Ndume ya ce akwai yiwuwar ya iya ficewa daga APC Hoto: Senator Mohammed Ali Ndume
Source: Twitter

Sanatan ya bayyana hakan ne yayin da ake tattaunawa da shi a shirin 'Prime Time' na tashar Arise tv.

Kara karanta wannan

Ana murnar kafa ADA, El Rufai ya hango kalubalen da za a iya fuskanta a INEC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ali Ndume ya taɓo batun shuga haɗaka

Ndume, wanda ya sha sukar shugaban ƙasa a baya-bayan nan, ya ce ya halarci wasu tarurruka da dama da shugabannin jam’iyyun adawa ke yi da nufin kafa haɗaka domin kayar da Tinubu a zaɓen 2027.

Sanatan ya bayyana cewa har yanzu yana nuna jinkiri wajen shiga wannan ƙawance, domin yana da imanin cewa Tinubu zai iya gyara Najeriya.

"Ina da masaniya game da haɗakar jam’iyyun adawa. Na halarci wasu daga cikin tarurrukansu. Har yanzu ina da yaƙinin cewa wannan shugaban ƙasan na iya gyara abubuwa, amma idan ya gaza, hakan na iya tilasta min ficewa. Jirgin da aka cika shi da yawa sai ya nutse."
“Suna ta nemana da tayin shiga, amma na shaida musu cewa ba zan so na fita daga wuta na faɗa cikin wata wutar ba. Sai na tabbatar."
“Ina da amannar cewa Tinubu zai iya zama shugaban ƙasa mai nasara, wannan shi ne burina tun da farko."

Kara karanta wannan

ADA: Atiku ya gana da 'yan Kanyywood, 'yan siyasar Arewa kan sabuwar tafiya

"Amma idan ya cigaba da tafiya haka, wannan jirgi, ko da kuwa an cika shi da wasu mutane ko gwamnoni, ana jefa jam’iyyar APC ne cikin haɗari, kuma hakan na iya haddasa nutsewar jirgin."
"Kamar yadda shugaban ƙasa ya ce, akwai gurbi a cikin jirgin. Amma idan aka cika jirgin fiye da ƙima, lallai zai iya nutsewa, kuma idan hakan ta faru, kowa zai halaka."

- Sanata Ali Ndume

Ndume ya sake magana kan ficewa daga APC
Ndume ya ce 'yan hadaka na zawarcinsa Hoto: Senator Mohammed Ali Ndume
Source: Facebook

Sauya-sheka: Ndume ya soki masu shigowa APC

Ndume ya kuma caccaki dalilan wasu mutane da ke sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki, inda ya bayyana hakan a matsayin tsoro da kwaɗayi.

"Yawancin mutane ba sa shigowa jam’iyyar bisa ƙa’ida ko aƙida, sai dai saboda siyasar tsoro da kwaɗayi. Wannan kuwa ba abu bane mai kyau."

- Sanata Ali Ndume

Ndume ya faɗi gwamnan da zai sa ya zauna a APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya bayyana gwamnan da zai sa ya ci gaba da zama a jam'iyyar APC.

Ali Ndume ya bayyana cewa zai ci gaba da zama a APC matuƙar gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, yana cikinta.

Sanatan Kudancin Bornon ya ba da tabbacin cewa muddin Zulum yana nan a APC, to shi ma ba zai raba gari da ita ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng