Rikicin PDP: Bukola Saraki Ya Fadi Lokacin Farfadowar Jam'iyyar

Rikicin PDP: Bukola Saraki Ya Fadi Lokacin Farfadowar Jam'iyyar

  • Shugaban kwamitin sulhu na PDP, Bukola Saraki, ya nuna ƙwarin gwiwa kan cewa za a warware rikicin jam'iyyar
  • Bukola Saraki ya bayyana cewa PDP za ta dawo da ƙarfinta nan da shekarar 2027, domin ana buƙatar adawa a tsarin dimokuraɗiyya
  • Tsohon shugaban na majalisar dattawa ya kuma yabawa mambobin jam'iyyar kan yadda suke fitowa domin yin rajista

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kwara - Tsohon shugaban majalisar dattawa kuma shugaban kwamitin sulhu na PDP, Dr. Abubakar Bukola Saraki, ya yi magana kan rikicin jam'iyyar.

Bukola Saraki ya bayyana cewa yana bakin ƙoƙarinsa wajen ceto jam’iyyar, tare da tabbatar da cewa PDP za ta dawo da ƙarfinta a shekarar 2027.

Saraki ya tabo batun rikicin PDP
Saraki ya ce PDP za ta farfado kafin 2027 Hoto: @bukolasaraki
Source: Twitter

Bukola Saraki ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata hira da manema labarai a ofishinsa da ke unguwar Ajikobi, Ilorin, babban birnin jihar Kwara, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Sanata Barau ya sake raunata tafiyar Kwankwasiyya a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban majalisar dattawan ya yi bayanin ne bayan ya gana da dubban mambobin jam’iyyar da suka halarci wurin domin sake yin rajista, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Me Bukola Saraki ya ce kan rikicin PDP?

Ya bayyana ƙwarin gwiwa cewa jam’iyyar na da isasshen lokaci don warware rikicin shugabanci da ke addabarta, yana mai jaddada cewa ya ƙudiri aniyar kare dimokuraɗiyya ta gaskiya, wadda ke buƙatar ingantacciyar jam’iyyar adawa.

Saraki wanda yake cikin annashuwa, ya gode wa ƴan Najeriya bisa haƙurin da suka nuna da jam’iyyar PDP.

"Ina so na yi amfani da wannan dama na tabbatar wa da mambobinmu a faɗin ƙasa cewa muna bakin ƙoƙarinmu wajen ceton halin da jam’iyyar ke ciki."
"Muna da yaƙinin cewa za mu shawo kan wannan matsala. Muna da niyyar yin hakan. Domin muna da jajircewa wajen kare dimokuraɗiyya ta gaskiya, wadda ke nufin cewa dole ne a samu jam’iyyar adawa mai ƙarfi. Dole ne kowa ya sadaukar da kai don amfanin ƙasa."

Kara karanta wannan

"Zama daram": Sanata ya sha alwashin kin ficewa daga PDP, ya ambaci dalili

- Bukola Saraki

Game da aikin sake rajistar jam’iyyar da ke gudana, ya ce sun ƙara samun ƙwarin gwiwa ganin irin yadda mambobi suke fitowa.

Ya danganta nasarar aikin rajistar jam’iyyar da matsin tattalin arziƙin da jama’a ke fuskanta.

"Ina ganin matsalolin da mutane ke fuskanta a jihar nan, rashin tsaro, rashin aikin yi, yunwa da kuma rashin ingantacciyar gwamnati, su ne ke taimakawa wajen janyo mutane da dama su dawo cikin jam’iyyar PDP."
"Don haka muna da tabbacin cewa PDP za ta dawo da ƙarfinta a shekarar 2027."

- Bukola Saraki

Saraki ya yabawa aikin rajistar mambobin PDP
Saraki ya ce PDP za ta dawo da karfinta Hoto: @bukolasaraki
Source: Twitter

Saraki ya yabi jam'iyyar PDP

Saraki ya kuma jaddada cewa PDP ce kaɗai ingantacciyar jam’iyyar adawa, kuma tabbas tana fuskantar ƙalubale, amma ya ɗauki alhakin ganin ya ba da gudummawa wajen kawo ƙarshen matsalolin.

"Ina ganin martanin da nake samu daga abokan aiki na masu nuna cewa suna da shirin sasanta saɓanin da ke akwai da haɗa kai domin farfaɗo da jam’iyyar."

Kara karanta wannan

Mutuwa ta ƙara taɓa sarakunan Najeriya, Sarki na 2 ya rasu cikin awanni 24

- Bukola Saraki

Wike ya ce babu mai korarsa a PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya cika baki kan zamansa a jam'iyyar PDP.

Wike ya bayyana cewa babu wanda ya isa ya kore shi daga PDP wadda ya tsaya ya ba da gudunmawa mai tarin yawa.

Ministan ya kuma ba da tabbacin cewa zai ci gaba da zama a jam'iyyar wadda tun sa ya shige ta bai taɓa ficewa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng