Yadda Hadakar Atiku, El Rufai Za Ta Iya Kawar da Tinubu a 2027', Umar Ardo
- Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Adamawa a ƙarƙashin inuwar SDP a zaɓen 2023, Umar Ardo, ya yi magana kan shirin kifar da Bola Tinubu
- Umar Ardo wanda ya taba sha'awar takarar shugaban kasa ya ce haɗakar adawa za ta iya kawar da Tinubu a 2027 idan aka bi hanyar da ta dace
- Ya bayyana cewa kafa sabuwar jam'iyya ita ce mafita idan har ƴan haɗakar suna son samun nasara a babban zaɓen 2027 da ake tunkara
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Adamawa a ƙarƙashin jam’iyyar SDP a zaɓen 2023, Umar Ardo, ya yi magana kan haɗaka don kawar da Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Dr. Umar Ardo ya bayyana cewa akwai yiwuwar kifar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 muddin ƴan adawa suka kafa sabuwar jam’iyyar siyasa.

Source: Facebook
Tsohon ɗan takarar gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin Morning Show na gidan talabijin na Arise Tv a ranar Laraba, 4 ga watan Yunin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace shawara aka ba ƴan haɗaka?
Umar Ardo wanda ƙwararren mai tsara dabarun siyasa ne kuma mai jigo a tafiyar ƙungiyar League of Northern Democrats (LND), ya nuna ƙwarin gwiwa dangane ɗunƙulewar ƴan adawa a inuwa ɗaya.
Sai dai ya amince cewa haɗakar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ke jagoranta na fama da rashin daidaituwar ra’ayi.
Ya yi watsi da ra’ayin haɗaka ta shiga wata jam'iyya, yana mai jaddada cewa kafa sabuwar jam’iyya ce za ta bayar da wata tabbatacciyar dama ta karɓar mulki.
"Idan gaba ɗaya ƴan adawa suka haɗu suka amince da kafa sabuwar jam’iyya, akwai babban fata na samun nasara a kan Shugaba Tinubu a 2027."

Kara karanta wannan
Tinubu ya ƙara ƙarfi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya haƙura da neman mulki a 2027
“An kafa kwamitoci biyu a cikin haɗaka, ɗaya don duba yiwuwar haɗewa da wata jam’iyya da ake da ita a yanzu, ɗaya kuma don nazarin yiwuwar rajistar sabuwar jam'iyya."
"Dukkanin kwamitocin sun kammala aikinsu, kuma daga abin da na gani, hujjar haɗuwa da wata jam’iyya ba ta da ƙarfi.
- Umar Ardo

Source: Facebook
Umar Ardo ya nuna ƙwarin gwiwa kan haɗaka
Umar Ardo ya jaddada cewa nasarar haɗakar za ta dogara ne bisa amfani da dabarar da ta dace.
"Idan aka ɗauki hanyar da ta dace da kuma shawarwari nagari, ina da yaƙinin cewa samun nasara abu ne wanda zai yiwu."
- Umar Ardo
Ƙungiyar LND ta kafa sharaɗin shiga haɗaka
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar LND wacce Malam Ibrahim Shekarau ke jagoranta ta yi magana kan shiga haɗakar jam'iyyun ƴan adawa.
Ƙungiyar LND ta buƙaci su Atiku Abubakar da sauran ƴan haɗaka su kafa sabuwar jam'iyya don tunkarar zaɓen 2027.
LND ta bayyana cewa kafa sabuwar jam'iyya ce kawai abin da zai sanya ta shiga haɗakar ta ƴan adawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
