Sabon Rikici: Wike Ya Kwatanta Gwamna Fubara da 'Dan da Ya Gujewa Ubansa
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce ba zai iya sasantawa da Simi Fubara ba sai an shigo da sauran ɓangarorin da ke cikin rikicin siyasar Ribas
- Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi, inda ya zargi gwamna Simi Fubara da haɗa kai da abokan gabansa domin kawo masa cikas
- Wike ya ce nadamar da Fubara ke nunawa ba ta da tushe, yana mai kwatanta shi da ɗan da ya juya wa uba baya bayan an yi masa duk wani alheri
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ba zai iya yin sulhu da gwamnan Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, ba tare da shigar da sauran masu hannu a rikicin ba.
Hakan na zuwa ne yayin da ake fatan shawo kan rikicin jihar musamman lura da yadda Fubara ya fara yabon Wike.

Source: Facebook
Wike ya fadi hakan ne a wata hira da aka yi da shi kai tsaye a Channels TV, inda ya bayyana cewa sulhun ba zai yi tasiri ba idan ba a shigo da ‘yan majalisar dokoki da shugabannin jam’iyya ba.
Rikicin Ribas ya samo asali ne daga sabani tsakanin Wike da Fubara kan iko da tsarin siyasa a jihar, wanda ya jawo rabuwar kai a majalisa da kuma shigowar shugaba Tinubu cikin lamarin.
Wike ya fadi sharadin sulhu da Fubara
Wike ya tabbatar da cewa sulhu tsakanin shi da Fubara ba zai yiwu ba idan aka kau da kai daga sauran masu ruwa da tsaki da ke cikin rikicin ba.
Premium Times ta rahoto Wike ya ce:
“Za a yi sulhu ba tare da ‘yan majalisar dokoki ba? Za a yi sulhu ba tare da shugabannin jam’iyya ba?"
Ya bayyana cewa Fubara ya zo gidansa tare da gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, da tsohon gwamna Olusegun Osoba, amma tun daga wannan rana bai sake ganinsa ba.
"Fubara tamkar ɗan da ya ci amanar uba ne,' Wike
Don bayyana irin radadin da yake ji, Wike ya kwatanta kansa da uba da ya yi wa ɗa komai amma ya dawo da makami domin kashe shi.
Wike Ya ce:
“Kana tunanin yadda uba ke wahala ya kai ɗansa makaranta, ya ciyar da shi, ya koya masa tarbiyya. Sai kuma dare ɗaya, ɗan ka ya dawo da bindiga, wai so yake ya kashe ka.”
Ya kara da cewa wannan lamari ba zai gushe a zuciyarsa cikin sauki ba, domin nadama kadai ba ta isa ta share irin wannan ciwon zuciyar ba.

Source: Facebook
A karshe, Wike ya zargi Fubara da haɗa kai da mutanen da suka nemi hana shi zama gwamna, yana mai cewa su ne suka kai karar Fubara gaban EFCC.
An gargadi Tinubu kan alaka da Wike
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon hadimin shugaba Goodluck Jonatahan, Reuben Abati ya zargi Nyesom Wike da rashin ladabi.
Dr. Abati ya ce Wike ya saba cin mutuncin wadanda suka taimake shi a baya a siyasance bayan ya samu mukami.
A karkashin haka ya gargadi shugaba Bola Tinubu da ya yi taka tsantsan wajen hulda da ministan domin gujewa abin da zai iya faruwa a gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


