APC Ta Yi Gyara kan Batun ba 'Yan Majalisu Tikitin Takarar 2027 Kai Tsaye
- Jam’iyyar APC ta bayyana rashin jin dadin wani rahoto da ke cewa ta ba duk ‘yan majalisar tarayya tikiti sake takara ba tare da hamayya ba
- Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Felix Morka, ya ce rahoton ba ya da tushe kuma ya kamata a yi watsi da shi domin ba gaskiya ba ne
- Baya ga karyata labarin, Felix Mokwa ya ce masu yada labarin na yin haka ne domin tayar da husuma da jawo rudani a APC mai ci tun 2015
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jam’iyyar APC ta ce rahoton da ke yawo cewa jam’iyyar ta ba duka ‘yan majalisar tarayya damar sake tsayawa takara kai tsaye ba tare da fafatawa ba karya ne tsagwaronta.
A cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na jam’iyyar, Felix Morka, ya fitar a ranar Talata, ya bayyana rahoton a matsayin labarin bogi da aka kirkira don rudin jama’a.

Source: Facebook
Sanarwar, wacce aka wallafa a shafin X na jam'iyyar NNPP a ranar Talata ta kuma ja hankalin jama'a a kan su yi fatali da wannan labarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta karyata zancen ba 'yan majalisu takara
Jaridar The Cable ta wallafa cewa jam'iyya mai mulki ta APC ta ce hankalinta ya kai kan wani labari dake cewa ta sahalewa 'yan majalisunta su koma kai tsaye, kuma hakan bai yi mata dadi ba.
Sanarwar ta ce:
“An jawo hankalin jam’iyyar APC kan wani rahoto da ke yawo da taken ‘APC ta ba ‘yan majalisar tarayya tikitin takara kai tsaye’, wanda ke yawo kamar wutar daji a kafafen sada zumunta."
"Wannan rahoto ƙarya ne kuma ba shi da tushe ko makama. Bai fito daga jam’iyyarmu ba kuma ya kamata a yi watsi da shi baki ɗaya.”

Source: Facebook
APC ta kuma bukaci 'ya'yanta da al’ummar kasa gaba ɗaya da su yi watsi da rahoton, tana mai cewa ba gaskiya ba ne kuma an kirkire shi ne domin a hada husuma..
Jama'a sun yi martani ga APC
Wasu daga cikin masu bibiyar APC a shafukan sada zumunta sun bayyana shakku a kan yadda jam'iyyar ta karyata rahoton sahalewa 'yan majalisa su sake neman kujerunsu a 2027.
Da yawa daga cikinsu na ganin idan babu rami, menene ya kawo rami, suna masu cewa akwai maganar bayar da tikitin ba tare da hamayya ba.
Jane bond ta ce:
"Jam’iyyar APC ta ce rahotannin da ke cewa tana bayar da tikitin takara kai tsaye ba gaskiya ba ne. Abin dariya, saboda abu ɗaya tilo da ke tafiya kai tsaye a APC shi ne: Cn hanci, gazawa."
"Wannan jam’iyya ba dandalin siyasa ba ce, sai dai wata cutar da ba ta da magani da ke yiwa dimokuraɗiyya illa a Najeriya, tana lalata hukumomi, da tattalin arziki."
"A duk lokacin zaɓe, burinsu shi ne “canji,” amma abin da muke samu kuwa: canjin farashin mai, canjin darajar Naira, da kuma canjin rayuwa, amma zuwa mafi muni."
APC ta soki Atiku, El-Rufa'i da Amaechi
A baya, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi kaca-kaca da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi, da tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai,.
Jam'iyyar ta yi zargin cewa manyan yan siyasan na kokarin hada adawa ne kawai domin kashin kai, amma ba saboda suna da kishin talakawan Najeriya ko kadan ba.
APC ta kara da zargin cewa dukkanin jagororin sun rike madafun iko na sama da shekaru 20, amma ba su iya wani katabus ta fannin ci gaba ko rage karfin talauci a yankunansu ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


