Da Gaske Natasha Ta Yi Alwashin Kifar da Tinubu a 2027? Bayani Ya Fito
- Natasha Akpoti ta karyata zargin da ke cewa tana yunkurin rusa gwamnatin Bola Tinubu da ake cewa ta fifita kabilar Yarbawa
- Tace ba ta taɓa furta cewa tana adawa da gwamnatin Bola Tinubu ba, tana mai cewa tana da kyakkyawar alaka da shugaban kasar
- Sanata Natasha ta ce rikicinta da Shugaban Majalisa, Godswill Akpabio ne kawai, ba wai da dukkan 'yan majalisa ko shugaban kasa ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya a majalisar dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta musanta zargin cewa tana da wata manufa ta rusa gwamnatin Bola Tinubu.
Haka zalika Sanatar ta wanke kanta daga zargin cewa ta ce gwamnatin Tinubu na fifita kabilar Yarbawa.

Source: Facebook
Rahoton jaridar Tribune ya nuna cewa Sanata Natasha ta yi maganar ne yayin hira da manema labarai a kasar Amurka.

Kara karanta wannan
Akpabio: Sanata Natasha ta saki sabon bidiyo kan yadda ake 'wawure kuɗi' a Majalisa
Martani Natasha na zuwa ne bayan wata mata mai suna Sandra Duru ta bayyana cewa Natasha ta shaida mata cewa tana aiki domin ganin bayan gwamnatin Tinubu mai fifita Yarbawa.
A wata hira da ta yi da wata yar jarida ‘yar Najeriya da ke Amurka, Adeola Fayehun, Natasha ta ce ba ta taɓa yin irin wannan magana ba, tana mai jaddada cewa babu kabilanci a ranta.
'Ba na nuna kabilanci a rayuwa' — Natasha
Natasha ta bayyana cewa ba ta da wata manufa ta kabilanci, tana mai cewa tana mutunta kowace kabila da al’umma a Najeriya.
Jaridar The Guardian ta rahoto cewa Natasha ta kara da cewa kasancewarta yar Najeriya da kuma Ukraine ya sa ba ta da dalilin raina kowace kabila.
Ta ce masu daukar nauyin Sandra Duru ne suka bullo da wannan zargi saboda suna jin cewa tana samun karɓuwa daga ‘yan Najeriya, ciki har da na cikin gida da na kasashen waje.

Kara karanta wannan
'Gwamnatinka ta jefa talakawa a masifa,' Kungiyar Yarbawa, Afenifere ta soki Tinubu
Ta bayyana cewa tana da kyakkyawar alaka da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, inda ta ce ma akwai lokacin da ta gana da shi kafin ta kawo bukatar binciken kamfanin Ajaokuta.
Kifar da Tinubu: Me yasa a ake zargin Natasha?
Natasha ta bayyana cewa wata magana da Shugaban Majalisa, Godswill Akpabio, ya yi ne ya janyo duk wannan zargi.
Ta ce Akpabio ya shaida wa mijinta cewa yana sane da cewa tana ganawa da shugaban kasa, kuma hakan ya ba shi haushi.

Source: Twitter
Ta ce ko da yake tana cikin jam’iyyar adawa, amma tana aiki da shugaban kasa a wasu lamura masu muhimmanci domin cigaban kasa.
Natasha ta jaddada cewa rikicinta ba da shugaban kasa ba ne, ko da majalisa ba, kawai rikicin da ke tsakaninta da Akpabio ne ya janyo wasu ke yunkurin bata mata suna.
Gwamnatin tarayya ta maka Natasha a kotu
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Bola Tinubu ta maka Sanata Natasha Akpoti a gaban kotun tarayya a Abuja.
Rahotanni sun nuna ministan shari'a ne ya gabatar da karar da ake zargin Natasha da raina wasu manyan jami'an gwamnati.
An bayyana cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello na cikin shaidun gwamnatin tarayya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng