Ministan Buhari Ya Raba Hanya da Tinubu da Ganduje, Ya Fice daga Jam'iyyar APC

Ministan Buhari Ya Raba Hanya da Tinubu da Ganduje, Ya Fice daga Jam'iyyar APC

  • Tsohon Ministan Muhalli a gwamnatin Muhammadu Buhari, Mohammed Abdullahi, ya fice daga jam’iyyar APC da ya shafe shekaru a ciki
  • Ya bayyana cewa dalilin ficewarsa daga jam’iyyar na da nasaba da "dalilai na kashin kai", ba tare da bayyana matakin siyasa da zai dauka ba
  • Ficewar tsohon ministan tarayyan na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara shirin sake tsara siyasa domin zaben shekarar 2027 a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon Ministan Muhalli a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, Mohammed Abdullahi, ya ajiye mukaminsa na zama dan jam’iyyar APC bisa dalilai na kashin kai.

Rahoto ya nuna cewa wannan mataki ya jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasar jihar Nasarawa da ma kasa baki daya.

Ministan Buhari
Ministan Buhari ya fita daga APC. Hoto: @MohdHAbdullahi
Source: Twitter

APC ta rasa tsohon ministan muhalli

Kara karanta wannan

'Akwai babbar barazana ga APC,' Babban lauya ya fadi abin da zai kifar da Tinubu

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa tsohon ministan ya bayyana ficewarsa ne cikin wata wasika da ya rubuta wa jam'iyyar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohammed Abdullahi ya rubuta wasikar ne ga shugaban jam’iyyar APC na gundumar Uke da ke karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa.

Ya ce ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi na yin aiki da kuma irin hadin kai da aka nuna masa.

Abdullahi ya taba rike mukamin Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG) a lokacin mulkin tsohon gwamna Umaru Tanko Al-Makura, kafin daga bisani Buhari ya nada shi minista a gwamnatinsa.

Wace jam'iyya tsohon ministan zai koma?

Duk da ficewarsa daga jam’iyyar, Abdullahi bai bayyana wata sabuwar jam’iyya da zai shiga ba, sai dai ya ce ya fice ne saboda dalilai na kashin kansa.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan siyasa da dama ke canza sheka domin shirin tsayawa takara a babban zaben 2027.

Vanguard ta wallafa cewa wani makusanci ga tsohon ministan mai suna Samuel Akala ya tabbatar da ficewar a wata tattaunawa da manema labarai a Lafia.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 36 sun nuna damuwa bayan ambaliya ta ruguza gidaje da mutane a Neja

Ministan Buhari
Mohammed Abdullahi bai fadi jam'iyyar da zai koma ba. Hoto: @MohdHAbdullahi
Source: Twitter

Ya kuma nuna yiwuwar cewa tsohon ministan zai bayyana sabuwar jam’iyya da zai shiga a nan gaba, domin cimma burinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar Nasarawa a 2027.

'Yadda 'yan siyasa ke sauya sheka a Najeriya

Wannan ficewa ta Abdullahi na zuwa ne a daidai lokacin da wasu fitattun ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa ke komawa APC gabanin zaben 2027.

Matakin na iya kawo sauyi a siyasar jihar Nasarawa, musamman duba da tasirin da tsohon ministan ke da shi tun daga lokacin da ya kasance SSG har zuwa matsayin minista.

Ko da yake ba a bayyana cikakken dalilin ficewarsa ba, wasu na ganin hakan na da nasaba da sababbin tsare-tsaren siyasa da suke gudana a Najeriya.

Siyasar Najeriya: Atiku ya ziyarci El-Rufa'i

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

Atiku Abubakar ya ziyarci El-Rufa'i ne domin tattauna batutuwan da suka shafi siyasa da cigaban Najeriya.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da sauya sheka a Najeriya ta tattauna maganar hadakar 'yan adawa domin tunkarar APC da Bola Tinubu a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng