Kudin Mazaɓa: Tinubu Ya ba Kowane Ɗan Majalisar Tarayya Naira Biliyan 1? Bayanai Sun Fito

Kudin Mazaɓa: Tinubu Ya ba Kowane Ɗan Majalisar Tarayya Naira Biliyan 1? Bayanai Sun Fito

  • Majalisar Tarayya ta karyata ikirarin da tsohon ɗan takara ya yi cewa ana ba kowane ɗan Majalisa Naira biliyan 1 a matsayin kudin ayyukan mazaɓa
  • Mai magana da yawun majalisar wakilai, Hon. Akin Rotimi ya ce zargin ba gaskiya ba ne, ƙarya ce da aka kirkira domin rikita jama'a
  • Ya ce wanda ya fito ya yi maganar ya tsaya takara ne bai ci ba shiyasa ya ɗauko wannan hanyar da nufin jawo hankalin jama'a kafin zaɓen 2027

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar Wakilan Tarayya ta musanta rahoton da ake yaɗawa cewa ana ba kowane mamba Naira biliyan 1 a matsayin kuɗin ayyukan mazaɓa.

Mai magana da yawun Majalisar Wakilai, Hon. Akin Rotimi, ya bayyana zargin da ake yadawa a matsayin ƙarya mara tushe, da aka kirkira domin ruɗa jama'a.

Kara karanta wannan

"Ba ɗan ƙunar baƙin wake ba ne," Ministan Tinubu ya gano mutumin da ya tashi 'bam' a Abuja

Majalisar Wakilai.
Majalisar Wakilai ta musanta zargin ana ba kowane ɗan majalisa N1bn Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

Hon. Rotimi ya yi wannan bayani ne a ranar Juma’a a birnin Abuja a wani taron tattaunawa da aka shirya kan dokar FOI, kamar yadda jaridar Guardian ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Rotimi, wanda ya fara yaɗa wannan ƙarya shi ne wani tsohon ɗan takarar kujerar majalisa, wanda ya fadi zaɓe a baya, kuma yanzu yana ƙoƙarin daga sunansa don samun tagomashi a zaɓe na gaba.

Yadda aka fara zargin ƴan Majalisa na samun N1bn

A wani bidiyo da ke ta yawo kwanan nan a soshiyal midiya, wani jigon APC a jihar Osun, Ayodele Asalu, ya yi iƙirarin cewa tun bayan cire tallafin fetur, gwamnatin Tinubu ta ƙara kuɗin ayyukan mazaba.

Ya ce bayan hawan Tinubu da cire tallafi, shugaban kasa ya ƙara kuɗin ayyukan mazaɓa daga naira miliyan 200 zuwa biliyan 1 ga ’yan majalisar wakilai.

Haka nan ya ce ana ba kowane sanata a Majalisar Dattawa akalla Naira biliyan 2 a matsayin kuɗin ayyukan mazaɓa kowace shekara.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ƙara ƙarfi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya haƙura da neman mulki a 2027

Da gaske ana ba kowane ɗan Majalisa N1bn?

Da yake martani kan wannan ikirari, Rotimi ya jaddada cewa wadannan bayanai karya ne, kuma an faɗe su ne da manufar rikita jama’a.

Ya ce majalisar wakilai ta yi shiru a farkon lamari ne domin ba wa ’yan majalisa damar bayyana gaskiya kai tsaye ga mutanen mazabunsu cikin yaren da suke fahimta.

Majalisar Wakilai.
Zargin ana ba kowane Ɗan Majalisar Wakilai akalla N1bn ba gaskiya ba ne Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

Rotimi ya ce:

“Kwanan nan, ko makonni biyu da suka wuce, an saki bidiyon wani mutum da ya tsaya takarar kujerar majalisa amma bai yi nasara ba, amma yanzu yana kokarin amfani da ƙarya wajen samun tasiri kafin zaɓe na gaba.
"Ya ce kowane ɗan majalisa ana ba shi Naira biliyan 1, wannan ba gaskiya bane. Wasu ma suna tunanin cewa ana ba mu wannan kuɗi ne kai tsaye ko ma kowane wata, ba tare da sun fahimci yadda tsarin kasafin kuɗi ke aiki ba.

An tono yadda aka cusa ayyuka a kasafin 2025

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar BudgIT, ta ce ta gano karin ayyuka da aka cusa a kasafin kudin 2025 da Majalisar Dokoki ta kasa ta amince da shi.

Kara karanta wannan

APC: Yahaya Bello ya yi magana da aka ce zai buga da Tinubu a zaben 2027

Kungiyar mai zaman kanta ta bayyana cewa ta gano ayyuka 11,122 da darajarsu ta kai Naira tiriliyan 6.93 da aka cusa a kasafin wannan shekara ba tare da bayani ba.

Rahoton da kungiyar ta wallafa ya nuna cewa wannan kaso na ayyuka da aka saka ba bisa ka’ida ba ya kai 12.5% na jimillar kasafin 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262