Hadaka: Atiku Ya Ziyarci El Rufa'i, Sun Tattauna Makomar Najeriya

Hadaka: Atiku Ya Ziyarci El Rufa'i, Sun Tattauna Makomar Najeriya

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kai wa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ziyara a gidansa da ke Abuja
  • Ziyarar na zuwa ne bayan El-Rufa’i ya fara fafutukar kawar da APC da shigar sa cikin shirye-shiryen kawo karshen gwamnatin Bola Tinubu a 2027
  • Ana ginin cewa El-Rufa’i da Atiku Abubakar na ƙara kusantar juna bayan sauya shekar El-Rufa’i zuwa jam’iyyar SDP mai adawa a kwanakin baya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A daren Litinin, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya kai ziyara ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, a gidansa da ke Aso Drive, Abuja.

Atiku ya samu rakiyar Dujiman Adamawa, Alhaji Musa Halilu Ahmed yayin da suka gana da El-Rufa’i a wani zaman da aka bayyana da cike da girmamawa da tattaunawa mai ma’ana.

Kara karanta wannan

Hasashen El Rufai ya tabbata, SDP mai kokarin kwace mulki ta shiga Matsala

Atiku
Atiku ya ziyarci El-Rufa'i a Abuja. Hoto: @Rasheethe
Source: Twitter

Hadimin Atiku Abubakar ya wallafa a X cewa sun tattauna ne kan ci gaban ƙasa da makomar siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ziyarar ta janyo ce-ce-ku-ce duba da cewa El-Rufa’i ya fice daga jam’iyyar APC, tare da bayyana sabuwar dangantakarsa da Atiku Abubakar, babban ɗan adawa a Najeriya.

Siyasar 2027: El-Rufa’i da Atiku sun ƙara kusanci

Ziyarar Atiku zuwa gidan El-Rufa’i na ƙara tabbatar da alakar siyasa da ke ƙarfafa tsakaninsu, musamman bayan ficewar El-Rufa’i daga APC zuwa jam’iyyar SDP.

El-Rufa’i wanda ya kasance babban jigo a kamfen ɗin Bola Tinubu a 2023, ya janye daga goyon bayan gwamnatinsa mai ci.

Atiku
Atiku da El-rufa'i yayin taron 'yan adawa a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Duk da cewa ya musa hakan, ana rade radin cewa rashin ba shi mukamin minista da aka yi masa alkawari na daga cikin abubuwan da suka fusata El-Rufa’i.

A halin yanzu, ana ci gaba da danganta shi da masu adawa da Bola Tinubu, ciki har da Atiku, wanda ke jajircewa wajen ganin an fitar da APC daga mulki a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Daga fara maganar hakaɗa a ADC, ana zargin gwamnan APC ya fara shirin komawa

Abin da Atiku ya tattauna da El-Rufa'i

A cewar wata sanarwa daga bangaren Atiku, zaman da suka yi da El-Rufa’i ya gudana cikin lumana da girmamawa.

Rahoto ya ce sun tattauna kan ci gaban ƙasa da bukatar haɗin gwiwa wajen ceto Najeriya daga matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro.

Duk da cewa ba a bayyana cikakken bayani kan abin da suka tattauna ba, majiyoyi sun ce ba za a rasa nasabar zaman da batun hadakar 'yan adawa ba.

Sabuwar alaka tsakanin Atiku da El-Rufa’i na iya haifar da guguwa a siyasar Najeriya, musamman ma a fagen jam’iyyun adawa da ke neman kifar da APC a 2027.

Kotu ta ci tarar Nasir El-Rufa'i a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa wata kotun tarayya a Kaduna ta ci tarar tsohon gwamna Nasir El-Rufa'i N900m.

An shigar da Nasir El-Rufa'i kara ne kan tsare wasu dattawan Kaduna a shekarar 2019 bayan kashe Sarkin Adara.

Bayan El-Rufa'i, Legit ta rahoto cewa kotun ta ci tarar wasu jami'an 'yan sanda N10m kan tsare dattawan ba bisa ka'ida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng