Jam'iyyar APC Ta Sake Yi Wa PDP Lahani a Fagen Siyasar Najeriya
- Jam'iyyar PDP ta rasa wasu manyan ƴan siyasa da ke cikinta bayan sun sauya sheƙa zuwa APC mai mulki a jihar Sokoto
- Ƴan siyasar sun samu tarba daga wajen sanata mai wakiltar Sokoto ta Tsakiya, Aliyu Magatakarda Wamakko a gidansa da ke Sokoto
- Sanata Wamakko ya nuna farin cikinsa kan matakin da ƴan siyasar suka ɗauka na shigowar jam'iyyar APC mai ci a jiha da kasa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Sanata mai wakiltar Sokoto ta Arewa, Sanata Aliyu Wamakko ya karɓi wata babbar tawagar ƴan siyasa da suka sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
Sauya sheƙar ƴan siyasar dai ta zama wata gagarumar nasara ga jam’iyyar APC mai mulki a jihar Sokoto.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce waɗanda suka sauya sheƙar sun haɗa da shugabannin ƙungiyar ƴan Kasuwa ta jihar Sokoto, a ƙarƙashin jagorancin shugabansu, Alhaji Chika Sarkin-Gishiri.
Wamakko ya karɓi masu sauya sheƙa daga PDP
An karɓe su ne cikin jam’iyyar APC a hukumance ta hannun Sanata Wamakko a gidansa da ke Sokoto a ranar Talata, a wani ɓangare na bikin cika shekaru biyu da gwamnatin Gwamna Ahmed Aliyu ke mulki.
Wamakko, wanda tsohon gwamna ne kuma fitaccen ɗan siyasa a jihar, ya bayyana godiyarsa ga matakin da ƴan kasuwar suka ɗauka na shiga jam’iyyar mai mulki, tare da tabbatar musu da cewa za a dama da su a gwamnati.
"Babu wani dalili da zai sa a bar ƴan kasuwa a baya. Tunda kun amince da yin aiki tare da gwamnati, muna da yaƙinin cewa abubuwa da dama za su samu ci gaba."
- Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko
Sanatan ya yaba da irin sauye-sauyen da ke faruwa a jihar Sokoto ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu, inda ya bayyana cewa a bayyane suke kuma suna da tasiri sosai, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Ya bayyana aikin gyaran babbar kasuwar Sokoto, wata muhimmiyar cibiya ta kasuwanci da gobara ta shafa a baya, a matsayin shaida ga ƙudirin gwamnati na bunƙasa harkar kasuwanci.
Haka kuma, ya bayyana shirin gwamnatin jihar na ƙaddamar da manyan shirye-shiryen ba da tallafin kuɗi domin ƙarfafa ƙanana da matsakaitan sana’o’i a fadin jihar.

Source: Facebook
Meyasa ƴan kasuwa suka koma APC?
A nasa jawabin, Alhaji Chika Sarkin-Gishiri ya bayyana sauya sheƙar a matsayin babbar asara ga jam’iyyar PDP a jihar, yana mai jaddada cewa manyan ƴan kasuwa masu tasiri sun sauya akalarsu zuwa APC.
“Mun yanke wannan shawara ne saboda muna da niyyar bada gudummawar gaske ga ci gaban jihar. Mun yi amanna da tsare-tsaren APC, kuma mun shirya bayar da cikakken goyon baya."
- Alhaji Chika Sarkin-Gishiri
PDP za ta hukunta masu haddasa rikici a jam'iyyar
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban riƙo na jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya yi magana kan rikicin da ya addabi jam'iyyar.
Umar Damagum ya bayyana cewa suna sane da waɗanda suke haddasa rikici a jam'iyyar PDP don wargaza ta.
Shugaban na PDP ya bayyana cewa ba za su yi nasara ba, kuma a shirye suke su kore su daga jam'iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

