Shugaban PDP Ya Fadi Matakin Dauka kan Masu Haddasa Rikici a Jam'iyyar

Shugaban PDP Ya Fadi Matakin Dauka kan Masu Haddasa Rikici a Jam'iyyar

  • Muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya yi jawabi a wajen taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) na jam'iyyar da aka gudanar
  • Umar Damagum ya bayyana cewa rikicin da ya dabaibaye PDP wasu mutane na cikin jam'iyyar ne suka assasa shi
  • Shugaban na PDP ya bayyana cewa suna sane da irin waɗannan mutane kuma a shirye suke da su kore su daga cikin jam'iyyar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya yi magana kan masu haddasa rikici a jam'iyyar.

Umar Damagum ya ce za a kori dukkan mambobin da ke haddasa rikici a cikin jam’iyyar PDP.

Umar Damagum
Damagum ya ce za a hukunta masu haddasa rikici a PDP Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Umar Damagum ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja, yayin taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) na jam’iyyar, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

PDP ta taso Tinubu a gaba, ta fadi babban tsoronsa a zaben 2027

Jam'iyyar PDP ta daɗe ba ta yi taron NEC ba

A cewar sashe na 31(4) na kundin tsarin mulkin PDP, ya wajaba a gudanar da taron NEC sau ɗaya a cikin kowane watanni uku.

Sai dai PDP ba ta gudanar da irin wannan taro ba tun daga watan Afrilun shekarar 2024.

Tun daga shekarar 2022, jam’iyyar PDP ke fama da rikice-rikicen cikin gida, wanda hakan ya sa da dama daga cikin mambobinta suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar mai mulki ta APC.

Me shugaban PDP ya ce kan rikicin jam'iyyar?

Umar Damagum ya bayyana cewa jam’iyyar PDP na da hanyoyin cikin gida da take bi don shawo kan matsalolinta.

“Ina so na sake jaddada cewa ɗaya daga cikin kyawawan halaye na PDP shi ne tana da tsari na cikin gida da take amfani da shi wajen warware duk wata matsala da wani ko wasu ke haddasawa, ko da kuwa ba ɗan jam’iyyar ba ne, kuma muna sane da hakan."

Kara karanta wannan

"Ba za ta sabu ba": Gwamnonin PDP sun nuna yatsa ga gwamnatin tarayya

"Wannan taro ɗaya ne daga cikin hanyoyin warware matsalolin. Mutane na daga waje suna jiran ganin ko za mu iya shawo kan waɗannan matsaloli da muka jefa kanmu a ciki, wasu kuma daga wasu wurare ke tayar da su."
"Amma da taimakon Allah, muna ci gaba da cin galaba. Za su kawo mana cikas, mu kuma za mu kau da su har sai mun nuna musu hanyar fita."

- Umar Damagum

Umar Damagum
Damagum ya ce za su kori masu haddasa rikici a PDP Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Umar Damagum ya ce kafin babban taron ƙasa da za a gudanar a ƙarshen shekarar 2025, za a sake gudanar da taron NEC sau uku.

Gwamnonin PDP sun zargi gwamnatin tarayya

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnonin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya sun yi sabon zargi kan gwamnatin tarayya.

Gwamnonin na PDP sun zargi gwamnati da bin masu hanyoyi don takura musu tare da kitsa rikici a cikin jam'iyyun adawa.

Sai dai, duk da hakan gwamnonin sun sha alwashin cewa ba za su bari bori ya hau ba, domin za su ci gaba da jajircewa da nuna haɗin kai wajen gudanar da manufofin PDP.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng