'Wike Annoba ne': Sule Lamido Ya Fadi Mutum 2 da Ya Kamata a Kore Su daga PDP
- Sule Lamido ya ce ba zai sake halartar tarukan PDP ba har sai an kori Nyesom Wike da Samuel Ortom daga jam’iyyar kan cin amana
- Lamido ya soki yadda PDP ke ci gaba da karɓar Samuel Anyanwu a matsayin sakatare, duk da cewa yankinsa ya riga ya yi watsi da shi
- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa Wike bala’i ne, yana kokarin rusa jam’iyyar da ta haife shi, bayan kwace mata hedikwarta a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Babban jigo a kwamitin zartaswar PDP na ƙasa (NEC), kuma tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya yi barazanar ƙauracewa taron jam’iyyar.
Sule Lamido ya ce ba zai sake halartar tarukan PDP ba har sai an kori ministan Abuja, Nyesom Wike da tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom daga jam'iyyar.

Source: Twitter
The Nation ta ruwaito cewa tsohon ministan harkokin wajen ya kaurace wa taron NEC karo na 99 na jam’iyyar da aka gudanar a Legacy House, Abuja ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sule Lamido ya nemi a kori Wike daga PDP
Sule Lamido ya kuma nuna rashin jin daɗinsa kan ci gaba da karɓar Sanata Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar na kasa, duk da cewa yankinsa ya riga ya yi watsi da shi.
Ko da yake Wike da Anyanwu ba su halarci taron ba, Samuel Ortom wanda yanzu mamba ne a kwamitin amintattu na PDP (BoT), ya halarci zaman.
Ortom ya halarci taron sanye da hula ta gargajiyar Tiv da farar babbar riga, kuma ya iso wurin taron tare da gwamnan Bauchi kuma shugaban gwamnonin PDP, Bala Mohammed.
Sule Lamido, wanda shi ma mamba ne a kwamitin BoT na jam’iyyar, ya ce ya kamata a kori Wike da Ortom daga PDP saboda cin amanar jam'iyyar a zaɓen 2023.
“Ga wani mutum da PDP ta ɗaukaka, ta ba shi kima, amma yanzu ya juya mata baya yana ƙoƙarin rusa jam’iyyar da ta haife shi. Wike annoba ne, gaskiya,” inji Sule Lamido.
'Ba zan halarci taro Wike na wurin ba' - Sule
Sule Lamido ya ƙara da cewa:
“Abin da yake yi ba ɗabi’ar Najeriya ba ce, kuma ba na Afirka ba ce. Domin kawai don yana da wani muradi sai ya ɗauki komai da zafi yana cutar da jam’iyyar da ya fito daga cikinta?

Source: Facebook
“Ka rufe sakatariyar jam’iyyar da ta ba ka suna, ta ba ka dama – duk irin fushinka, wannan kamar rusa gidanka ne. Sai ya zo yana da’awar cewa shi ne ya rika ciyar da jam’iyyar.
“To amma idan ɗa yana ciyar da mahaifiyarsa, sai hakan ya nuna cewa dole sai mahaifiyar ta zama baiwa gare shi ba saboda kawai yana bata tufafi?”
“Yaya zan zauna a wani zama na kwamitin amintattu tare da Ortom ko Wike domin tattauna makomar PDP? Ko kuma wani da yankinsa ya yi watsi da shi amma ana tilasta shi kan sauran jam’iyyar? Wannan ai maganar banza ce."

Kara karanta wannan
Gwamnonin PDP sun 'zagaya' Wike, Ministan ya kara dagula lamuran rikicin jam'iyyar
- Sule Lamido.
Abin da zai faru da Najeriya idan PDP ta rushe
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sule Lamido ya yi gargadin cewa Najeriya za ta faɗa hannun 'yan kama karya idan har PDP ta shuɗe daga siyasar ƙasar.
Tsohon gwamnan na Jigawa ya ce PDP ita ce ginshiƙin dimokuraɗiyyar Najeriya, kuma rasa ta na nufin rushewar tsarin mulkin dimokuraɗiyya baki ɗaya.
Duk da rikice-rikicen cikin gida da ke cikin PDP, Lamido ya jaddada cewa ba zai fice daga jam’iyyar ba, yana ganin tana da muhimmiyar rawa a Najeriya.
Asali: Legit.ng

