"Ba Za Ta Sabu ba": Gwamnonin PDP Sun Nuna Yatsa ga Gwamnatin Tarayya

"Ba Za Ta Sabu ba": Gwamnonin PDP Sun Nuna Yatsa ga Gwamnatin Tarayya

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta gudanar da taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) a babban birnin tarayya Abuja
  • A wajen taron gwamnonin PDP sun zargi gwamnatin tarayya da yin amfani da wasu dabaru don kawu rabuwar kai a tsakanin ƴan adawa
  • Gwamnonin sun bayyana cewa ba su bari irin waɗannan dabarun su yi tasiri a kansu ba domin za su ci gaba da jajircewa wajen haɗa kawunansu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnonin jam’iyyar PDP sun zargi gwamnatin tarayya da amfani da dabarun tsoratarwa tare da maida su saniyar ware.

Gwamnonin na PDP sun sha alwashin ƙin yarda da irin waɗannan matakai tare da jajircewa wajen ci gaba da gudanar da mulki na gari.

Gwamnonin PDP
Gwamnonin PDP sun zargi gwamnatin tarayya Hoto: @DOlusegun, @AgbuKefas
Source: Twitter

Sun bayyana hakan ne yayin taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) karo na 99 na jam’iyyar PDP da aka gudanar a ranar Talata a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Shugaban PDP ya bayyana matakin dauka kan masu haddasa rikici a jam'iyyar

Gwamnonin PDP sun yi zargi kan gwamnatin tarayya

Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, kuma gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, wanda ya yi jawabi a wajen taron, ya bayyana irin ƙalubalen da jam’iyyar da mambobinta ke fuskanta a halin yanzu.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa gwamnatin da ke mulki ta haifar da yanayi na musamman da ke cike da matsaloli, tunzurawa da kuma canje-canjen yanayin siyasa, rahoton TheCable ya tabbatar.

Ya ce PDP na fuskantar ƙalubalen sauya sheƙa daga wasu mambobinta da kuma tattaunawar kafa ƙawance da wasu, wanda hakan ya shafi wasu ƴan jam’iyyar.

Sai dai ya jaddada cewa jam’iyyar za ta ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai da jajircewa ga manufarta.

“Duk da waɗannan matsaloli da muke fuskanta, mambobinmu sun ci gaba da kasancewa masu kishin jam’iyya da jajircewa."
"Babu irin nau’in tsoratarwa ko ƙoƙarin jan hankali da mu a matsayinmu na zaɓaɓɓun gwamnoni, ba mu fuskanta ba. Amma duk da haka, mun tsaya tsayin daka."

Kara karanta wannan

Suswam: Tsohon gwamna ya lisaafo mutum 2 da suka jawo rikicin PDP

- Gwamna Bala Mohammed

Gwamnonin PDP
Gwamnonin PDP sun halarci taron NEC Hoto: @seyimakinde
Source: Twitter

PDP ta bambanta da sauran jam'iyyu

Bala ya ƙara da cewa haɗin kan da ke tsakanin ƴaƴan PDP shi ne abin da ke bambanta su da sauran jam’iyyu da ya bayyana da cewa sun tarwatse, inda suke da rassa daban-daban masu rikici.

“Sauran jam’iyyu sun rabu gida biyu, suna da bangarori daban-daban da ke rikici tsakaninsu. Amma babu shakka, PDP na nan daram, muna tafiya tare da hadin kai."

- Gwamna Bala Mohammed

Suswam ya lissafo matsalolin PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam, ya yi magana kan rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar PDP.

Gabriel Suswam ya bayyana cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da shugaban riƙo na PDP, Umar Damagum, su ne matsalar jam'iyyar.

Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa bai kamata a ɗora laifi ga ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, kan rikicin da ya daɗe yana ci wa jam'iyyar tuwo a ƙwarya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng