Karon Farko bayan Shiga APC, Gwamna Sheriff Ya Shiga Aso Villa, Ya Gana da Tinubu
- Shugaba Bola Tinubu ya sanya labule da gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori a fadar Aso Rock, da misalin karfe 3:45 na ranar Talata
- An ce wannan shi ne karon farko da Shugaba Tinubu da Gwamna Sheriff suka gana a Aso Rock tun bayan da gwamnan ya koma APC
- Ana ganin cewa gwamnan Deltan ya gana da Tinubu ne domin tabbatar da barinsa PDP zuwa APC da kuma kulla kawance mai karfi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, a Fadar Aso Rock, Abuja.
Wannan ce ziyarar farko da Gwamna Sheriff Oborevwori ya kai Aso Rock tun bayan sauya sheƙarsa daga PDP zuwa APC mai mulki.

Source: Twitter
Gwamnan Delta ya gana da Shugaba Tinubu
Jaridar Punch ta ruwaito cewa gwamnan ya isa fadar shugaban ƙasa da misalin karfe 3:45 na yammacin ranar Talata, 6 ga Afrilu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kuma rahoto cewa Gwamna Sheriff ya ziyarci shugaban kasar shi kadai, ba tare da rakiyar mukarraban gwamnatinsa ba.
Manyan jami’an gwamnatin tarayya ne aka ce suka tarbi gwamnan jihar Deltan kafin ya sanya labule da shugaban ƙasa Tinubu.
Taron na ranar Talata shi ne ganawar farko da gwamnan ya yi da shugaban ƙasa tun bayan komawarsa jam’iyyar APC mai mulki.
Zuwan gwamnan Aso Rock bayan sauya sheka
Ko da yake ba a samu cikakkun bayanai game da taron ba, amma ana ganin ziyarar a matsayin tabbatar da sauyin shekarsa ta baya-bayan nan da kuma alamar ƙulla ƙawance da gwamnatin tarayya ta APC.
A ranar 23 ga Afrilu, 2025, Oborevwori ya zama gwamnan jihar Delta na farko da ya bar PDP zuwa wata jam'iyyar adawa, tun daga 1999.
Magabacinsa, Ifeanyi Okowa, mataimakin gwamna, Monday Onyeme, kwamishinoni, shugabannin ƙananan hukumomi, da magoya baya sun koma APC bayan taron sirri a Asaba.
Idan ba a manta ba, Ifeanyi Okowa shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a babban zaɓen 2023.

Source: Twitter
Abin da Tinubu ya ce bayan ganawa da Sheriff
Jim kadan bayan wannan ganawa, shugaban kasa, Tinubu ya wallafa a shafinsa na X cewa:
"A yau, na gana da gwamnonin jihohin Delta da Ekiti a fadar shugaban kasa. Mun tattauna muhimman batutuwa game da damammakin samun ci gaba mai ɗorewa a jihohinsu da kuma matsalolin da suke fuskanta.
"Gwamnatinmu ta ci gaba da jajircewa wajen tallafawa da haɗa kai da gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi don samar da ci gaba mai ɗorewa a faɗin Najeriya.
"Na daɗe da dora dukkanin yakinina a kan ƙasarmu mai ƙima, Najeriya, kuma dole ne mu yi aiki tukuru don samar da makoma mai kyau ga dukkan 'yan Najeriya. Wannan shine alkawarinmu na Renewd Hope."
Duba sanarwar a nan kasa:
Asali: Legit.ng

