An Faɗi Ranar da Ake Son Dawo da Fubara bayan Taso Tinubu a Gaba, Ya Nemi Afuwa

An Faɗi Ranar da Ake Son Dawo da Fubara bayan Taso Tinubu a Gaba, Ya Nemi Afuwa

  • Wasu rahotanni sun ce an taso shugaban kasa, Bola Tinubu a gaba bayan sanya dokar ta-ɓaci a Rivers
  • Gwamna Siminalayi Fubara ya sauko daga matsayinsa ya nemi gafara daga Nyesom Wike a gidansa dake Abuja don sasanta rikicin siyasar jihar
  • Bayan ganawa da shugaba Tinubu, Fubara ya nuna nadama tare da neman zaman lafiya ba tare da goyon bayan dattawan Rivers ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Bayan ya fahimci yadda rashin mulki ke yi wa mutum illa, Gwamna Fubara ya kuduri aniyar neman sulhu da Nyesom Wike domin zaman lafiya.

A ranar 18 ga Afrilu, rahotanni sun nuna cewa Fubara ya ziyarci Wike a gidansa dake Abuja domin neman yafiya da sulhu.

Ana rokon Tinubu ya dawo da Fubara mulki
An taro Bola Tinubu a gaba ya dawo da Fubara mulki a Rivers. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Nyesom Ezenwo Wike.
Source: Facebook

Yadda Fubara ya zabi sulhu kan siyasar Rivers

Kara karanta wannan

Faɗan daba: Ɗan siyasa ya haɗa kan matasa da ba su ga maciji a Kano, an samu mafita

Rahoton Vanguard ya ce dalilin da yasa ya zabi shiga da wasu jiga-jigan siyasar Yarbawa ba dattawan Rivers ba, abu ne da za a iya fahimta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fubara ya gane cewa babu hanyar da za a bi don warware rikicin siyasar Rivers face ta hanyar sulhu na gaskiya da rashin makirci.

Wannan shi ne dalilin da yasa ya yanke shawarar samun zaman lafiya wurin shigar dattawan Rivers cikin lamarin ba.

Tsoma bakin shugaban kasa da batun kafa dokar ta baci ne ya dakile yunƙurin tsige Fubara da kawo karshen aikinsa na siyasa.

Babu bayani kai tsaye kan abin da suka tattauna Fubara ya tattauna da Tinubu amma majiyoyi sun ce ganawar ta kai ga wata yarjejeniya da zata taimaki Tinubu a 2027.

Bayan ganawa da shugaban kasa, Fubara bai tsaya ba, ya ziyarci Wike da nadama yana neman gafara kan abubuwan da suka faru.

Tinubu na shan matsin lamba kan dawo da Fubara
An bukaci Tinubu ya dawo da Fubara a karshen watan Mayu. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Ranar da ake son Tinubu ya dawo da Fubara

Ana rade-radin cewa Tinubu na fuskantar matsin lamba daga manyan 'yan Najeriya domin ya dawo da Fubara kafin 29 ga Mayu.

Kara karanta wannan

Wike ya zargi gwamna Fubara da jawo wulakanta matar Tinubu a Rivers

A cewar mai magana da yawun IRA, Ann Kio Briggs ta ce dawo da Fubara ranar 29 ga Mayu zai faranta ran mutanen Rivers.

Ta ce:

“Ya kamata a dawo da shi ranar Dimokradiyya domin ya hadu da sauran gwamnoni wajen bikin cika shekaru biyu a kujerar mulki.”

Briggs ta ce mutanen Rivers za su gode wa Tinubu idan ya dawo da Fubara, domin rikicin ya ci su fiye da kima.

Shugaban INC, Farfesa Benjamin Okaba, ya ce Tinubu zai kafa tarihi idan ya dawo da Fubara ranar 29 ga Mayu da cike shakku.

Ya ce:

“Ziyarar Fubara ga shugaban kasa da Wike abin maraba ne. Shugaban kasa zai kafa tarihi idan ya dawo da shi da wuri."

Kunyata Remi Tinubu: Wike ya soki Fubara

Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Ezenwo Wike ya bayyana ficewar wasu mata daga wurin taron da uwargidan Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu, ta jagoranta a matsayin abin kunya.

Nyesom Wike ya ce hakan rashin girmama ofishin shugaban kasa ne, yana mai neman afuwar Bola Tinubu bisa lamarin da ya faru a jihar Rivers.

Lamarin ya auku ne yayin wani taron tallafa wa mata da ofishin uwargidan Shugaban Kasa ya shirya, wasu mata suka fice daga wurin suna zanga-zanga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.