"Sai Yanzu Ka San Yana da Kima?" El Rufa'i Ya Tunawa Ganduje Ya Kira Buhari Habu na Habu

"Sai Yanzu Ka San Yana da Kima?" El Rufa'i Ya Tunawa Ganduje Ya Kira Buhari Habu na Habu

  • Tsohon jigo a APC, Nasir El-Rufa’i, ya ce kaucewa akidar jam’iyyar ce ta tilasta masa sauya sheka domin neman mafita ga talakawa
  • Haka kuma, ya caccaki jagororin APC, inda ya zarge su da watsi da tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, na tsawon lokaci
  • Ya zargi shugaban jam’iyyar APC na yanzu, Abdullahi Umar Ganduje, da rashin girmama Buhari da kuma furta munanan kalamai a kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya sake nanata cewa jam'iyyar APC ce ta tilasta masa ya bar cikinta, ta hanyar kaucewa akidar da aka gina ta a kai.

El-Rufa'i, wanda guda ne daga cikin mutanen da suka sanya hannu wajen samar da hadakar jam’iyyu da ta kafa APC, ya ce jam’iyyar ta sauya daga turbar da aka kafa ta a kai.

Kara karanta wannan

Ganduje ya ce Kwankwaso zai bar NNPP, ya dawo jam'iyyar APC

Ganduje
Etl-rufa'i ya tusa Ganduje a gaba Hoto: Nasir El-Rufa'i/Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

A wata hira da ya yi da DW Hausa, El-Rufa'i ya ce ya yi iya bakin kokarinsa wajen dawo da jam’iyyar kan turbar gaskiya, amma abin ya ci tura.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa jam’iyyar APC ta shafe sama da shekaru biyu ba tare da ta gudanar da babban zaben cikin gida ba, duk da muhimmancin hakan ga tsarin jam’iyya.

Nasir El-Rufa’i ya tsine wa jam'iyyar APC

Tsohon jagora a jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan Kaduna sau biyu, Nasir El-Rufa’i, ya bayyana cewa ya tsine wa APC, kuma ya bar ta da bakin duniya.

A hirar da ya yi, El-Rufa’i ya ce:

“Ni jam’iyyar ce ta bar ni, saboda haka dole ne na samu wata jam’iyya da nake gani tana kamanta irin akidar da muka tsaya kai, mu 37 da muka sa hannu aka yi rajistar APC."
Ni uba ne ko uwa ga APC, amma ko ɗa ne ka haifa ya fandare, ka yi iyakar kokarinka, ka yi addu’a, ka yi komai da komai, ya kasa – dole ka tsine masa, ka bar shi da duniya. To, na tsine wa APC, na bar ta da duniya.”

Kara karanta wannan

Atiku: Gwamna ya fadi dalilin Gwamnonin PDP na watsi da kawancen jam'iyyu

El-Rufa’i ya caccaki Abdullahi Ganduje

Nasir El-Rufa’i ya mayar da martani kan kalaman shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya ce tafiyar su El-Rufa’i wajen tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ba za ta yi tasiri ba.

El-Rufa’i ya ce tun da Buhari ya bar gwamnati, jagororin APC suka yi watsi da shi, sai bayan da suka fahimci ya fice daga APC zuwa SDP suka waiwayi tsohon shugaban.

Nasir
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

Ya ce:

“Ba Ganduje ba ne ya taba cewa Buhari Habu na Habu? Yanzu ne ya gane Buhari na da muhimmanci da girma?"
"Tun da Buhari ya bar gwamnati, sau nawa suka je neman shi? Sau nawa suka kira shi suna neman shawararsa a kan wani abu?"
Abin da ya kai su Ganduje wurin Buhari shi ne ganin cewa Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar, da wasu daga cikinmu sun kai masa gaisuwar Sallah – shi ke nan. Sai suka ruga da tsakar dare, suka hana ɗan tsoho bacci, suna matsa masa.”

Kara karanta wannan

Sanata Ndume na shirin ficewa daga APC ya haɗe da El Rufai a SDP? Ya yi bayani da bakinsa

Jagororin NNPP za su koma APC

A baya, mun wallafa cewa Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sanya labule da wasu fitattun ’yan majalisar jam’iyyar NNPP daga Kano.

Wannan ganawa ta ƙara zafafa rade-radin sauya sheƙarsu zuwa APC kafin babban zaɓen 2027, bayan sun samu matsala da tsagin Kwankwasiyya na NNPP.

Hadimin Ganduje, Aminu Dahiru Ahmad, ya ce taron yana cikin shirye-shiryen da wasu jiga-jigan NNPP ke yi na barin jam’iyyar mai mulki a Kano domin komawa APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel