Bayan Kalaman Zulum kan Tsaro, APC Ta Aika Muhimmin Sako ga Tinubu kan Zaben 2027

Bayan Kalaman Zulum kan Tsaro, APC Ta Aika Muhimmin Sako ga Tinubu kan Zaben 2027

  • Jam’iyyar APC, reshen jihar Borno ta bayyana goyon bayanta ga rade-radin da ake yi na tsayawar Shugaba Bola Tinubu takara a 2027
  • Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun jinjina wa Kashim Shettima, tare da yin kira ga Tinubu da ya sake daukarsa matsayin abokin takara
  • Shugabannin APC na Borno sun bukaci Tinubu ya ci gaba da zuba jari a aikin hakar mai da gine-ginen hanyoyi a Arewa maso Gabas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Jam’iyyar APC reshen jihar Borno ta bayyana goyon bayanta ga rade-radin tsayawar Shugaba Bola Ahmed Tinubu takara karo na biyu a 2027.

APC, ta aika muhimmin sako ga shugaban kasar, ta shaida masa cewa ya kwantar da hankalinsa, tana tare da shi komai runtsi a zaben mai zuwa.

Kara karanta wannan

'Hanya 1 ce': Atiku Ya Saɓa da Gwamnonin PDP kan Haɗaka da Tuge Tinubu a Mulki

APC reshen Borno ta yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027
Shugaban kasa Bola Tinubu tare da Kashim Shettima a yayin wani taro. Hoto: @officialSKSM
Asali: Twitter

APC reshen Borno ta amince da tazarcen Tinubu

Jam’iyyar mai mulki a Borno ta bukaci sake tsayar da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a matsayin abokin takarar Tinubu, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan matsaya ta fito ne daga taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC da aka gudanar a gidan gwamnatin Borno da ke Maiduguri,a ranar Lahadi.

A wata sanarwa da shugaban APC na jihar, Bello Ayuba, da sakataren jam’iyyar, Mustapha Loskuri, suka rattaba hannu, an yabawa Shettima bisa kishinsa da biyayyarsa ga Tinubu.

“Muna kira ga mataimakin shugaban kasa da ya ci gaba da nuna biyayya ga shugaban kasa tare da gudanar da aikinsa da gaskiya da rikon amana,” inji sanarwar.

Masu ruwa da tsakin jam'iyyar sun kuma nemi Shugaba Tinubu ya rike Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a neman wa'adi na biyu.

"Borno ta jam'iyyar APC ce" - Sanarwar Bello, Loskuri

Jam'iyyar APC, reshen Borno, ta kuma bayyana cikakken goyon baya da biyayya ga gwamnatin tarayya da ke ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Dakatar da Fubara: Mata sun cika tituna a Rivers suna zanga zanga

Haka kuma, jagororin jam'iyyar sun amince da manufofin “Renewed Hope” na gwamnatin Tinubu tare da yi masa da Shettima fatan samun nasara da kariyar Ubangiji.

Masu taron sun yanke shawarar cewa jihar Borno za ta ci gaba da kasancewa a karkashin APC, kuma ba za a yarda da kawance ko sauya sheka ba.

The Cable ta rahoto cewa an bukaci ‘yan jam’iyyar da su guji duk wani abu da zai bata sunan APC a jihar Borno ko kasa baki daya.

An nemi Tinubu ya tallafa wa Gwamna Zulum

APC ta nemi Tinubu ya sake rike Shettima matsayin abokin takararsa a 2027
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima (Hagu) tare da Shugaba Bola Tinubu (Dama). Hoto: @officialSKSM
Asali: Twitter

A wani bangare na taron, jiga-jigan APC sun nuna cikakken goyon baya ga Gwamna Babagana Umara Zulum, suna mai ba shi kwarin gwiwa da kada ya karkata hankalinsa daga yaki da ta’addanci da masu aikata laifuffuka.

Sun roki Shugaba Tinubu da ya ci gaba da marawa Gwamna Zulum baya a kokarin da ya ke na ganin an samar da tsaro a dukkanin kananan hukumomin jihar.

Kara karanta wannan

APC ta tabo batun ajiye Kashim Shettima, ta ba Shugaba Tinubu shawara

Manyan jam'iyyar sun kuma bukaci Tinubu da ya ci gaba da aikin hako danyen mai a yankin Arewa maso Gabas, musamman a Kolmani da gabar tafkin Chadi.

Bayan haka, sun roke shi da ya zuba jari a harkar gine-ginen hanyoyi a yankin Arewa maso Gabas don ƙara tabbatar da tsaro da cigaban yankunan.

Zulum ya caccaki ministan Tinubu kan tsaro

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya mayar da martani ga ministan labarai, Mohammed Idris, dangane da batun Boko Haram.

An ce Zulum ya yi martanin ne biyo bayan wani rahoto da ya nuna cewa ministan ya yi biris da damuwarsa kan matsalar tsaron jihar.

Gwamna Zulum ya ce ba ya son yin ja-in-ja da ministan yada labaran, amma yana da yakinin cewa Mohammed Idris bai fahimci irin halin da ake ciki a kasar ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng