Siyasar Kano: APC Ta Bukaci Ganduje Ya Taya Ta Kwato Kawu Sumaila daga NNPP

Siyasar Kano: APC Ta Bukaci Ganduje Ya Taya Ta Kwato Kawu Sumaila daga NNPP

  • Shugabannin APC a ƙananan hukumomi 16 na Kano ta Kudu sun roƙi Abdulrahman Kawu Sumaila ya dawo jam’iyyarsu
  • A bayanin da suka fitar, sun bayyana cewa Kawu Sumaila zai kara ƙima da kawo haɗin kai a jam’iyyar APC idan ya koma cikinta
  • Sun kuma nemi shugabannin jam’iyyar na jiha da ƙasa su shiga lamarin domin jawo Sumaila ya dawo tafiyar APC daga NNPP

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Shugabannin jam’iyyar APC na ƙananan hukumomi 16 da ke yankin Kano ta Kudu sun roƙi Sanata Sulaiman Kawu Sumaila da ya dawo jam’iyyar su.

Sun bayyana cewa sun bukace shi ne domin cigaban siyasar yankin da kuma ƙarfafa jam’iyyar a jihar Kano baki ɗaya.

Kawu Sumaila
An bukaci Kawu Sumaila ya koma APC. Hoto
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa kiran ya fito ne daga bakin shugabannin APC na ƙananan hukumomi da masu ruwa da tsaki a yankin yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a garin Albasu.

Kara karanta wannan

'Ciwon ido': Jigon PDP ya faɗi mutane 2 da za su zama barazana ga ƴan adawa a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Kawu Sumaila na wakiltar Kano ta Kudu ne a majalisar dattijai ƙarƙashin jam’iyyar NNPP tun bayan zaben 2023, inda ya sauya sheƙa daga APC zuwa NNPP kafin zaɓen.

'Saata Kawu Sumaila na da muhimmanci,' APC

Shugaban APC na ƙaramar hukumar Albasu, Iliyasu Hungu ne ya yi jawabi a madadin shugabannin jam’iyyar.

Iliyasu Hungu ya bayyana cewa Kawu Sumaila mutum ne mai ƙima da tasiri da zai taimaka wa APC matuƙa idan ya sauya sheka.

“Babu shakka, idan Sanata Kawu Sumaila ya amsa kiranmu ya dawo APC, zai ƙara daraja sosai ga APC kuma zai taimaka wajen haɗa kan ‘ya’yan jam’iyya a yankin,”

- Iliyasu Hungu

Ya ƙara da cewa koda ba dan APC ba ne a halin yanzu, Kawu Sumaila mutum ne da ke mu’amala da kowa cikin girmamawa ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa ba.

An nemi jagororin jam'iyyar APC su sa hannu

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya bugi kirji, ya fadi sabuwar jiha da gwamnatin Tinubu za ta kirkiro

Shugabannin sun roƙi manyan jam’iyyar kamar shugaban APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, Sanata Barau Jibrin, Abdullahi Abbas da su shiga lamarin don lallashin Sanata Sumaila.

Daily Post ta wallafa cewa Iliyasu Hungu ya ce:

“Muna da yakinin cewa Sumaila zai taka rawar gani matuƙa idan ya dawo jam’iyyar APC.
Mun rasa mutum mai kima kamar shi, amma muna fatan dawowarsa zai ƙarfafa mana gwiwa,”
Ganduje
An bukaci Ganduje ya sanya baki wajen dawo da Kawu Sumaila APC. Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Asali: Twitter

APC na buƙatar jagorori masu aminci

A cewar Iliyasu Hungu, APC na buƙatar shugabanni masu kishi kamar Sanata Sumaila, wanda kullum ke sadaukar da lokacinsa da dukiyarsa domin kyautata rayuwar al’umma.

Shugabannin yankin sun kammala da cewa dawowar Sumaila APC ba kawai za ta ƙarfafa jam’iyyar ba ne, har ma za ta haifar da haɗin kai da kwanciyar hankali a tsakanin al’ummar Kano ta Kudu.

Jam'iyyar APC za ta yi maraba da Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa mutane na bayyana ra'ayoyi kan rade radin cewa jagoran NNPP a Kano, Rabiu Kwankwaso zai sauya sheka.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Gwamnonin PDP sun bayyana matsayarsu kan hadaka don kayar da Tinuɓu

Mutane da dama na yada labarin cewa Sanata Rabiu Kwankwaso zai koma jam'iyyar APC kafin zaben 2027.

Duk da cewa har yanzu bai yi magana kan rade radin ba, Bashir Ahmad ya ce APC za ta yi maraba da Sanata Kwankwaso idan ya dawo cikinsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng