Za a Yi Gangamin Matasa Miliyan 5 domin Nuna Goyon Baya ga Tinubu

Za a Yi Gangamin Matasa Miliyan 5 domin Nuna Goyon Baya ga Tinubu

  • Ƙungiyar haɗin gwiwar matasan Kudu maso Gabas (COSEYL) ta sanar da shirin gudanar da gangamin goyon bayan Bola Tinubu da Orji Uzor Kalu
  • An shirya gangamin ne domin jaddada gamsuwa da shugabancin Tinubu da gudunmawar da Kalu ke bayarwa a mazabarsa ta Abia ta Arewa
  • Ƙungiyar ta bayyana cewa za ta haɗa matasa miliyan 5 daga shiyyar Kudu maso Gabas domin nuna cikakken goyon baya ga shugabannin biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Abia - Ƙungiyar matasan Kudu maso Gabas (COSEYL) za ta gudanar da gangamin matasa miliyan 5 a Abia domin nuna goyon baya ga Bola Tinubu da Sanata Orji Uzor Kalu a kan 2027.

Hakan na zuwa ne yayin da hankula suka fara karkata kan zaben 2027 duk da cewa ko shekara biyu ba a yi da rantsar da shugabannin da suka lashe zabe a 2023 ba.

Kara karanta wannan

Dakatar da Fubara: Mata sun cika tituna a Rivers suna zanga zanga

Tinubu
Za a yi gangamin goyon bayan Tinubu a Abia. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Shugaban ƙungiyar, Goodluck Ibem, da sakataren yaɗa labarai, Okey Nwaoru, ne suka rattaba hannu kan wata sanarwa da suka fitar a ranar Litinin, wacce jaridar The Sun ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gangamin matasa don goyon Tinubu a Abia

COSEYL ta bayyana cewa gangamin zai gudana ne a jihar Abia, kuma za a haɗa matasa miliyan 5 daga jihohin Kudu maso Gabas guda biyar domin tallata cigaban da gwamnati ke kawo wa.

Vanguard ta wallafa cewa kungiyar ta ce:

“Za mu kafa wani dandali na musamman domin bayyana irin ci gaban da Shugaba Tinubu da Sanata Kalu suka kawo,
"Musamman a fannin tituna, makarantun gwamnati, noma, da shirin ƙarfafa matasa,”

Ƙungiyar ta bayyana taron a matsayin matakin farko na tunkarar zaɓen 2027 tare da tabbatar da cewa shiyyar Kudu maso Gabas za ta kasance ginshiƙi mai ƙarfi na goyon bayan shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

APC ta tabo batun ajiye Kashim Shettima, ta ba Shugaba Tinubu shawara

'Ana jin dadin gwamnatin Tinubu,' COSEYL

COSEYL ta ce jama’ar shiyyar na jin daɗi da gamsuwa da yadda Sanata Kalu ke jagorancin wakilcin mazabar Abia ta Arewa.

Sun ƙara da cewa irin wannan namijin ƙoƙari ya taimaka wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai da amincewa da gwamnatin shugaba Tinubu, kuma hakan ne zai ba shi nasara a 2027.

COSEYL ta ce Tinubu na samun karbuwa

Ƙungiyar ta bayyana cewa ayyukan da shugaba Tinubu ke yi sun ɗaura Najeriya kan hanyar cigaba mai ɗorewa, kuma hakan ya ƙara jawo masa ƙaunar jama’a a shiyyar Kudu maso Gabas.

Sun ƙare da cewa a shirye suke su yi aiki kafada da kafada da shugabanni domin ci gaban Najeriya baki ɗaya.

Sanata Kalu
Matasan Abia za su yi gangamin goyon bayan Sanata Kalu. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Matan Rivers sun goyi bayan Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa wasu matan jihar Rivers sun yi zanga zangar goyon bayan matakin da Bola Tinubu ya dauka na dakatar da Simi Fubara.

Kara karanta wannan

2027: Sabuwar tafiyar Atiku da El Rufa'i ta fara samun karbuwa a Neja Delta

Matan sun fito kan tituna suna cewa sun fi bukatar zaman lafiya a kan duk wani dan siyasa da zai iya kawo tashin hankali a jihar.

A watan Maris da ya wuce ne shugaba Bola Tinubu ya dakatar da gwamna Fubara, mataimakiyarsa da majalisar dokokin jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng