‘Tinubu Za Su Taya Aiki’: Jigon PDP Ya Zargi Gwamnoni kan Fatali da Haɗakar Adawa

‘Tinubu Za Su Taya Aiki’: Jigon PDP Ya Zargi Gwamnoni kan Fatali da Haɗakar Adawa

  • Dele Momodu ya zargi wasu gwamnonin PDP da kin hadin gwiwa da sauran jam’iyyu, ya ce suna iya boyewa su marawa APC baya
  • Gwamnonin PDP sun fitar da wata sanarwa suna musanta yiwuwar hadakar jam’iyyu gabanin zaben shekarar 2027 da ke tafe
  • Momodu ya ce babu wata jam’iyyar adawa da za ta iya kada Tinubu idan ba su hade suka yi aiki tare kamar yadda APC ta yi a 2015 ba
  • Ya jaddada cewa idan gwamnonin PDP suka ki hada gwiwa, to hakan na iya nuna suna boye suna taimaka wa gwamnatin Tinubu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Dele Momodu wanda ya nemi tikitin shugaban kasa ya zargi gwamnonin jam'iyyar PDP da suka yi fatali da hadaka.

Momodu ya ce wasu gwamnoninsu na PDP da ke adawa da hadin gwiwa kafin 2027 suna iya marawa Bola Tinubu baya.

Kara karanta wannan

'Hanya 1 ce': Atiku Ya Saɓa da Gwamnonin PDP kan Haɗaka da Tuge Tinubu a Mulki

An gwamnonin PDP da shirin marawa Tinubu baya a 2027
Jigon PDP ya zargi gwamnonin PDP da neman goyon bayan Tinubu kan fatali da haɗaka. Hoto: PDP Governors' Forum, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Yayin wata tattaunawa a Arise TV, Momodu ya ce babu wata jam’iyyar adawa da za ta iya kada Tinubu a 2027 ita kadai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsayar gwamnonin PDP kan haɗaka a 2027

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, gwamnonin PDP sun ce ba za su yi hadaka da kowace jam’iyya ba kafin 2027.

Ana ta rade-radin cewa jam’iyyun adawa za su iya hade wuri guda domin fuskantar APC a babban zabe na gaba.

Gwamnonin na PDP sun kuma sake nuna goyon bayansu ga gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara wanda aka dakatar.

'Dan takaran PDP ya zargi gwamnonin jam'iyyar

Jigon PDP din ya shawarci jam’iyyun adawa su hade kamar yadda APC ta yi a 2015 har ta samu nasara a zaben wancan lokaci.

Ya ce:

“Shugabannin adawa sun kuduri aniyar yin aiki tare, gaskiya, Atiku ba zai iya shi kadai ba, haka Peter Obi da Kwankwaso ma.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Gwamnonin PDP sun bayyana matsayarsu kan hadaka don kayar da Tinuɓu

“Saboda haka, dole su nemi hanyar da za su rama wa APC, ta hanyar hada kan wasu jam’iyyu ciki har da APC kanta.
“Ina gwamnoninmu suna cewa ba su so hadaka, to hakan na nufin suna iya taimaka wa gwamnatin Tinubu a boye.
An zargi gwamnonin PDP da shirin taya Tinubu aiki a 2027
Jigon PDP, Dele Momodu ya caccaki gwamnonin jam'iyyar kan fatali da haɗaka. Hoto: Dele Momodu.
Asali: Twitter

Shawarar jigon PDP, Momodu ga yan Najeriya

Momodu ya shawarci yan Najeriya su dauki darasi duba da yadda yan siyasa suka ɗauki neman kujera a kasar inda ya ce azzalumai sun yi yawa, cewar TheCable.

Ya kara da cewa:

“Ya kamata mutane su dauki darasi daga tarihi; azzalumi ba ya jin tsoro sai da azzalumi kamar shi.
“Duk wani gwamna ko dan majalisa da ya yi yunkurin sauya sheka, zai iya fadawa a cikin teku mai zurfi."

Bode George ya fadi matsalolin PDP

Kun ji cewa kusa a PDP, Bode George ya yaba wa gwamnonin PDP bisa matakin da suka ɗauka na nesanta kansu da haɗakar jam'iyyun adawa.

Kara karanta wannan

Zamfara: Bayan kisan ɗan bindiga, miyagu sun ɗauki fansa, sun ƙona masallacin Juma'a

Jigon PDP ya bayyana cewa idan jam'iyyar ta sake kuskuren ba tsohon matainakin shugaban kasar takara, to karshenta ya zo.

Dattijon ya ce a tsarin dokokin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, Atiku ba shi da damar neman takarar shugaban kasa sai 2031.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng