Shugaban Majalisar Wakilai Ya Fadi Halascin da Tinubu Ya Yi Masa a Siyasance
- Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen ya bayyana irin faɗi tashin da ya yi kafin ya hau kan kujerar da yake kai a yanzu
- Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya goya masa baya duk da cewa bai san shi ba
- Shugaban majalisar wakilan ya kuma yabi gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani kan irin goyon bayan da ya ba shi a 2023
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya bayyana irin goyon bayan da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba shi.
Abbas Tajudeen ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya mara masa baya wajen neman shugabancin majalisar wakilai duk da cewa bai taɓa saninsa ba.

Asali: Twitter
Abbas Tajudeen ya bayyana haka ne yayin da yake rabon kayan tallafi ga mutanen mazaɓarsa a Zariya, jihar Kaduna, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane halasci Tinubu ya yi wa Abbas Tajudeen?
Shugaban majalisar wakilan ya bayyana cewa goyon bayan da shugaban ƙasan ya ba shi ya ta'allaƙa ne kawai bisa abin da ya karanta a kansa.
Ya kuma jinjinawa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, saboda goyon bayan da ya ba shi a lokacin da yawancin jami'an gwamnatin da ta gabata a jihar suka juya masa baya.
A cewar Abbas, Shugaba Tinubu shi ne mutum na farko kuma mafi girma da ya mara masa baya a burinsa na zama shugaban majalisar wakilai duk da cewa basu taɓa haɗuwa ba a baya.
"Shugaban ƙasa ya ba ni goyon baya bisa amannar da ya yi daga abin da ya karanta da kuma abin da ya ji game da ni. Bai taɓa haɗuwa da ni ba kafin ya mara min baya."
"Sunaye daban-daban aka gabatar masa, amma ya zaɓe ni ne saboda ya gamsu da cancanta ta."
- Abbas Tajudeen
Abbas Tajudeen ya godewa Uba Sani
Ya ce mutum na gaba da ya ba shi muhimmiyar gudunmawa a daidai lokacin da babu wanda ke tare da shi, shi ne Gwamna Uba Sani, wanda ya bayyana a matsayin ginshiƙi mai ƙarfi da ya tsaya masa a kowane hali.

Asali: Twitter
"Gwamna Uba Sani ya mara min baya a lokacin da yawancin jami’an gwamnatin da ta gabata a jihar Kaduna suka ƙi goyon bayana."
"Ya bayyana goyon bayansa tun kafin rantsar da shi, kuma ya tsaya a kan kalamansa bayan an rantsar da shi."
"Ya ku mutanen mazaɓa ta, ina so ku fahimci irin muhimmancin Gwamna Uba Sani a tafiyata ta siyasa. Don Allah ku miƙa irin goyon bayan da kuke bani zuwa gare shi."
"Ina so na maimaita abin da na faɗa a taron jiga-jigan APC na jihar Kaduna bara, ‘Ni Abbas Tajudeen, na ɗauki alƙawari cewa babu abin da zai raba ni da Gwamna Uba Sani komai ya faru, ko ruwa, ko rana, ni ne mutum na ƙarshe da zai tsaya masa.’"

Kara karanta wannan
"Zan ba gwamna mamaki," Sanata Nwoko ya yi ƙarin haske kan jihar da ake shirin ƙirƙirowa
- Abbas Tajudeen
Abbas Tajudeen ya faɗi ubangidansa a siyasa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya yi magana game da ubangidansa a siyasance.
Rt. Ho. Abbas Tajudeen ya bayyana cewa a tarihin siyasarsa, bai da wani mutum da zai nuna a matsayin ubangidansa a siyasa.
Shugaban majalisar wakilan ya bayyana cewa yana ɗaya daga cikin ƴan siyansan da ba su da ubangida.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng