Shugaban AMAC Ya Kara Jiƙa wa PDP Aiki a Abuja, Ya Sauya Sheka zuwa APC
- Shugaban ƙaramar hukumar birnin Abuja watau AMAC, Hon. Christopher Zakka Maikalangu ya fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC
- A wata sanarwa da ya fitar, ciyaman din na AMAC ya ce ya ɗauki wannan matakin ne domin ci gaban al'ummar da yake jagoranta
- A cewarsa, ba shi ne ɗan siyasa na farko da ya fara sauya sheka zuwa APC ba, ya ba da misali da ɗan takarar gwamna a jihar Anambra
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban karamar hukumar birnin tarayya Abuja (AMAC), Hon. Christopher Zakka Maikalangu, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Shugaban AMAC ya tabbatar da ficewa daga PDP zuwa APC a hukumance ranar Lahadi, 13 ga watan Afrilu, 2025.

Asali: Twitter
Leadership ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Kingsley Madaki ya fitar.

Kara karanta wannan
Sanata Ndume na shirin ficewa daga APC ya haɗe da El Rufai a SDP? Ya yi bayani da bakinsa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me yasa shugaban AMAC ya koma APC?
Maikalangu ya bayyana cewa al’ummar AMAC na rasa damammaki da dama daga gwamnatin tarayya saboda rashin kasancewa a jam’iyya mai mulki.
Shugaban ƙaramar hukumar ya ce APC ce kadai za ta ba shi damar cika burinsa da saukaka rayuwar mazauna AMAC.
“Na yanke wannan shawara ne bayan la’akari da bukatun al’ummata. Ba a zaɓe ni don na shugabanci al'ummar Najeriya ba, ni shugaban al'ummar yankin AMAC ne.
"Na lura cewa babu jam'iyyar da za ta kare muradun mutanena idan ba jam’iyya mai mulki watau APC ba.”
- Hon. Christopher Zakka Maikalangu.
Jam'iyyar APC za ta kare muradun AMAC
Ya bayyana idan bai haɗe da jam'iyya mai mulki ba, ƙaramar hukumar AMAC ba za ta samu ayyuka daga gwamnatin tarayya da tallafin da ya kamata ba.
"Na ɗauki wannan matakin ne domin cika muradan jama'a ta, ba na so mu ci gaba da zama waya jam'iyya daban, shiga APC zai kara kawo ci gaba ga al'ummar AMAC.

Kara karanta wannan
El Rufai ya yi magana, ya faɗi dalilin zuwan Atiku da manyan jiga jigai wurin Buhari
Maikalangu ya ambato wasu fitattun ‘yan siyasa da suka sauya sheka zuwa APC saboda dalilai makamantan haka.

Asali: UGC
Shugaban AMAC ya ambaci wasu jiga-jigai
Daga cikin yan siyasar da ya kira sunansu har da Prince Nicholas Ukachukwu wanda ke neman gwamna Anambra da Dr. Kingsley Kelachukwu Okoronkwo wanda ya bar LP zuwa APC saboda rikice-rikicen cikin gida.
Ya bayyana cewa babban jigon jam’iyyar APC, Hon. Gabriel Bravo Oluohu, ne ya shawarce shi da ya sauya sheka domin amfanin al’ummar AMAC.
“Duk da wannan mataki na iya zama mai amfani ga burina na siyasa, amma babban dalili shi ne ci gaban mutanena,” in ji shi.
Gwamna Alia na shirin barin APC?
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Hyacinth Iormem Alia na jihar Benuwai ya jaddada cewa ba shi da shirin ficewa daga APC zuwa wata jam'iyya.
Gwamnan ya ce ya karɓi ragamar mulkin jihar Benuwai ne bayan ya yi wa Allah, kansa da jama'a alkawarin kawo sauyi mai amfani.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa na aiwatar da manyan ayyuka kamar gina tituna masu tsawon fiye da kilomita 300, biyan albashi da fansho da sauran ayyukan ci gaban al'umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng